Hadiza Gabon ta mayarwa da wani saurayi da ya dade yana nemanta da aure martani

Hadiza Gabon ta mayarwa da wani saurayi da ya dade yana nemanta da aure martani

- Ga jaruman fina-finai, ba na Kannywood kacal ba, samun masoya masu tarin yawa wata al’ada ce

- Haka kuwa ya kasance da jaruma Hadiza Gabon, don wani bawan Allah ya bayyana cewa sunyi aure har da yara hudu amma a mafarkinshi

- Bayan dogon lokacin da ya dauka tare da tunatarwa da ta samu, jarumar tayi wa masoyinta bashir fatan alkhairi

Su dai dama jaruman fina-finai, ba na Kannywood kadai ba, duk a duniya sun kasance masu farin jini sosai a gurin mutanen gari. A wasu lokutan, jarumai mata kan samu goron gayyata zuwa cikin zuciya, wato dai ana yawan yi musu sakonnin tayin soyayya. Amma saidai ra’ayin jaruman bai fiye dacewa da na masoyan nasu ba.

Jaruma Hadiza Aliyu Gabon ta samu irin wannan sakon goron gayyata zuwa zuciyar wani, wanda ya nuna bukatar son aurenta. Duk da ba wannan ne karo na farko da jarumar ta fara samun irin wannan tayin ba daga kafafen sada zumuntar zamani.

Masoyin nata ya bayyana cewa yana tara kudin neman aurenta. Ya kuma bayyana cewa, duk da jarumar bata san dashi ba, a zuciyarshi yana ganin ta har sunyi aure tare da yara 4 kuma mata da maza.

KU KARANTA: Dare daya Allah kanyi Bature: Mutane sun hadawa Magajiya Danbatta taimakon Naira Miliyan 5 sanadiyyar Ja'afar Ja'afar

Kamar yadda yace, “Masoyiyata Hadiza Gabon, tana tunanin bata da saurayi. Amma ni can cikin mafarkina har munyi aure kuma mun haifa yara hudu, maza da mata.”

Amma kuma sai jarumar bata mayar mishi da martani ba har sai da wani bawan Allah yayi mata tuni da wannan masoyin nata.

A mayar da martanin da jarumar tayi wa mutumin, tace lallai yana da babbar zuciya kuma tana mishi fatan alheri.

“Lallai kana da babbar zuciya, ina maka fatan alkhairi Bashir.” Cewar Hadiza Gabon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel