Zamfara: Gwamnati ta ware N50m don gyaran sansanin 'yan bautar kasar jihar

Zamfara: Gwamnati ta ware N50m don gyaran sansanin 'yan bautar kasar jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware kudi har naira miliyan biyar don gyaran sansanin 'yan bautar kasa na jihar dake karamar hukumar Tsafe, a kasafin kudinta na 2020.

Kwamishinan habaka matasa da wasanni, Abdulkadir Buhari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Gusau a ranar Juma'a, bayan da ya kare kasafin kudin ma'aikatarsa a gaban majalisar jihar, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari yace, wadannan kudin za a yi amfani dasu ne wajen gyaran dakunan kwanan dake sansanin 'yan bautar kasar, gina sabon madafi na zamani da sauran gyare-gyaren da sansanin ke bukata.

"Kun san cewa a kowanne watanni uku, jihar na samun 'yan bautar kasa a kalla 2,000 da ake kawowa jihar. A don haka ne muka mayar da hankali wajen ganin walwalar masu hidimtawa kasar tare da habakasu a jihar", cewar kwamishinan.

DUBA WANNAN: Yadda mutane ke hijira zuwa kan duwatsu bayan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

A halin yanzu, mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Zamfara a hukumar fatattakar talauci, Rufa'i Chiroma, yayin kare kasafin kudin cibiyar na 2020, yace gwamnatin jihar ta tsara shirye-shirye kala-kala don ganin bayan talauci tare da tallafawa jama'ar jihar da 'yan ta'adda suka illata, ko kuma wadanda aka sace wa shanu.

"Kun san cewa, mutanenmu ballantana na karkara sun shiga mawuyacin hali sakamakon kalubalen da jihar ta fuskanta ta fannin tsaro. A halin zaman lafiyar nan da muka tsinci kanmu da daidaituwa, gwamnatin jihar na shirya yadda zata kirkiro shirye-shiryen rage talauci da rashin aikin yi," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel