Da duminsa: Buhari zai bar ofis kafin karshen 2020, sanadiyyar tsige shi da za ayi - Fasto

Da duminsa: Buhari zai bar ofis kafin karshen 2020, sanadiyyar tsige shi da za ayi - Fasto

- Wani babban Fasto a wata majami’a a jihar Legas ya bayyana manyan al’amuran da zasu faru a 2020

- Ya ce akwai yuwuwar a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma mugun rashin lafiya ya kwantar dashi

- Faston yace wasu ‘yan siyasa da attajirai a kasar nan su shiga taitayinsu, don wannan shekarar ba zata kasance mai kyau garesu ba

Babban faston Christ Foundation Miracle International Chapel, Lagos, Josiah Onuoha Chuckwuma yace akwai yuwuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga kujerarshi a karshen 2020.

Kamar yadda yace, Shugaban kasar zai tsallake wannan lamarin dake hararoshi ne matukar ya iya jurewa tare da jajircewa guguwar da zata tashi a karshen watan Nuwamba na 2020.

Chukwuma, wanda ya zanta da Chinedu Adonu a Enugu, yayi kira ga bulaliyar majalisar dattijai, Orji Uzor Kalu da kuma shugaban kamfanin jiragen sama na Air Peace, Allen Onyema da su gaggauta daukar mataki don tseratar da rayuwarsu da ta kasuwancinsu kafin su durkushe. Ya jaddada cewa, lamurransu na bukatar addu’a ne fiye da wasu al’amura na mutane.

Faston ya kara da cewa, yana hango wa ‘yan Najeriya hatsari kuma sai Buhari ya kiyaye. “Idan Buhari ya tsallake abinda Ubangiji ya nuna min, daga nan har zuwa karshen watan Nuwamba, toh tabbas zai karashe mulkinshi. Amma kamar yadda na gani, Buhari zai sauka daga karagar mulki ne ta hanyar tsigeshi ko kuma ciwo a 2020. Wannan shine abinda zan iya bayyanawa.” Cewar shi.

KU KARANTA: Kabilar Babur-Bura: Takaitaccen tarihinsu akan addini, aure da kuma yare

Faston ya kara da cewa, Ubangiji zai tona asirin fastoci ‘yan damfara ballantana kuma masu zubar da jini kuma suna ikirarin su na Allah ne. Hakan kuma zai faru da ‘yan siyasa matukar basu tuba ba. ‘Yan siyasa masu tarin yawa zasu rasa abubuwa masu muhimmanci a 2020. Zai fi idan suka koma ga Ubangiji.

“Za a samu tsanani a 2020. Zai fi idan ‘yan Najeriya suka roki Ubangiji rangwame, ta hakan ne kadai zai kawo sauki ga kasar da kuma ‘yan kasar. ‘Yan siyasa su sani, da yawa daga cikin masu ganin sun tara dukiya zasu fada tsananin yunwa. Wasu kuwa zasu kare a gidan fursuna ne kamar yadda tsohon gwamnan jihar Abia yayi. Zasu rasa nagartarsu.

“Na hango jam’iyyar APC ta sarke cikin matsananci rikici. Jam’iyyar zata tarwatse saboda yadda za a kasa shawo kan wannan rikicin. Rikicin zai sa manyan jam’iyyar su fara yi wa junansu fallasa da tonon asiri.” Cewar Faston.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel