Kabilar Babur-Bura: Takaitaccen tarihinsu akan addini, aure da kuma yare

Kabilar Babur-Bura: Takaitaccen tarihinsu akan addini, aure da kuma yare

- Bincike ya nuna cewa mutanen kabilar Babur Bura da na Luguda suna daga cikin wadanda suka yi hijira daga Yemen

- Wannan kabilar na da abubuwan mamaki a fannin aure, addinin, yare da sauran zamantakewa

- Ana samunsu ne a kananan hukumomi tare da garuruwa masu yawa na jihar Borno, Yobe, Adamawa da Gombe

Magabatan kabilar Babur Bura da na Luguda suna daga cikin wadanda suka yi hijirah daga Yemen ta Sudan zuwa yankin Chadi dake yankin Kanem Borno. Sune yaren Babur Bura dake Borno da jihar Adamawa.

Ana samun wannan kabilar ne a kananan hukumomin jihar Borno kamar haka: Garkida a karamar hukumar Gombi. Sanannun kauyuka kuwa da garuruwan da wannan kabilar suka fi yawaita sune Biu, Garkida, Kwajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa, Wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yamirshika ,Hyera ,Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam, Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdang, Bula taw ewe, Kogu Tashan Alade, Kida, da hang shang da sauransu.

Kabilar Bura suna fara neman aure ne tun bayan da aka haifa jinjirar yarinya. Masoyin kan wurga ganye a bukkar mahaifiyar jaririyar, idan an amince sai a sanar dashi. Ya kan fara bada toshi tare da yi wa mahaifinta hidima a gona.

Bayan isar ta aure, saurayin ko masoyin kan hada kai da abokanshi wajen daukota zuwa gidanshi. Daga nan sai a tsara sadaki da yadda bikin auren zai kasance.

Wannan kabilar sun yadda da al’adar fara kwanciya da mace a farin kyalle don gaon cewa ko macen ta kai budurcinta dakin mijinta. Idan bata kai ba, hakan ya kan zama abun kunya gareta da danginta.

KU KARANTA: Samarin da suke da mota sunfi zina da mata fiye da wanda ba su da ita - Binciken masana

Kafin isowar musulunci da addinin Kirista zuwa yankin a 1920, suna da addininsu mai suna Hyel ko Hyel-taku. Ana wakilta ruwa, duwatsu, tsaunika ko daji da abin bautarsu.

Yaren da wannan kabilar keyi na da hadi da na kasar Chadi da kuma yaren Biu-Mandara. Amma yaren yafi kamanceceniya da na Chibok, Marghi, Higg, Kilba da Bazza.

A halin yanzu ana samun wannan kabilar masu yawa a jihohin Borno, Adamawa, Gombe da Yobe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel