Jiragen ruwa 18 makare da man fetur da kayan abinci suna hanyar zuwa Najeriya - NPA

Jiragen ruwa 18 makare da man fetur da kayan abinci suna hanyar zuwa Najeriya - NPA

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, ta ce tana dakon zuwan wasu jirage 18 makare da man fetur da kayayyakin abinci da sauran kayayyaki kafin ranar 16 ga watan Janairun 2019.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa hukumar ta NPA ta bayyana hakan ne a cikin mujallarta mai lakabin 'Shipping Position' da aka rabawa manema labarai a Legas a ranar Alhamis.

A cewar mujallar, ana sa ran jiragen ruwan za su iso tashan jirgin ruwan Legas ne inda za su sauke kayayyakin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Bugu da kari, ta kuma ce jiragen na dauke da kayayyakin da ake sarrafawa daga danyen man fetur, kwantenoni, kayayyaki, kifi, gishiri, sukari, alkama, da sinadarin butane.

NPA ta ce tuni jirage 19 sun riga sun iso tashan jirgin suna jiran a sauke kayayyakin da suka dauko da suka hada da man fetur a wasu kwantenoni.

Kazalika, hukumar ta ce akwai wasu jiragen ruwa 20 da ke tashan ta Legas suna sauke iskar gas ta butane, sauran kayayyakin masarafi, kwantenoni, alkama mai yawa, sukari mai yawa, man fetur da mai kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel