Mutane 95 kadai suka fi Dangote kudi a duniya - Rahoto

Mutane 95 kadai suka fi Dangote kudi a duniya - Rahoto

Rahoton kafar yada labarai ta Bloomberg, ya nuna cewa arzikin shahararren dan kasuwar nan kuma mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya karu a shekarar 2019 da dala biliyan 4.3.

Hakan na nuni ga cewa a yanzu arzikin Dangote ya ‘dara dala bilyan 15 kenan, wannan ne kuma ya kai shi a matsayin na 96 a jerin masu arziki na dumiya.

Dangote wanda shi ne ya fi kowa kudi a Afrika, kuma bakar fatan da ya fi kowa kudi a duniya, ya samu karin makudan kudade ne cikin 2019 ta sanadiyar kasuwancin siminti, filawa da sukari.

Ya fara kasuwanci ya na da shekaru 21 a duniya. Ya kafa masana’antu da dama a Najeriya da wasu kasashe na Afrika.

A halin yanzu ya na gina katafariyar matatar mai da ake ganin ta na daga cikin mafi girma a duniya.

KU KARANTA KUMA: Siyasa rigar yanci: Dan majalisa ya baiwa mutane 220 mukamin masu bashi shawara

Ya fi kowa harkar kasuwancin siminti a Afrika, inda ya ke da masana’antu da dama a kasashe daban-daban na Afrika.

Idan za a kwatanta dala bilyan 15 da Dangote ya mallaka da naira, to sai a lissafa kowane dala bilyan daya na daidai da naira bilyan 360 kenan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel