Kungiyoyi sun maidawa Buhari martani bayan sakonsa na sabuwar shekara

Kungiyoyi sun maidawa Buhari martani bayan sakonsa na sabuwar shekara

Ana ta maganganu bayan jawabin shugaba Muhammadu Buhari na shiga sabuwar shekara. A jawabin, shugaban kasar ya kara tabbatar da cewa ba zai sake neman mulki ba.

Kungiyoyi irin su Afenifere, Ohanaeze, Arewa Youth Forum, PANDEF, da CAN da jam’iyyar adawa ta PDP sun soki jawabin shugaban kasar, su na kira ga gwamnatin APC ta kara kokaria bana.

Kungiyar Afenifere ta Yarbawa ta soki jawabin shugaban kasar, ta ce ya kamata gwamnatin Buhari ta maida hankali wajen yi wa tsarin Najeriya garambawul da karawa yankunan kasar karfi.

Sakataren yada labarai na kungiyar Yarbawan, Mista Yinka Odumakin, ya ce shugaba Buhari ya dade ya na yi wa mutanen Najeriya alkawura, don haka ya bukaci ya tsaya ya yi aiki a shekarar nan.

Ita kuma kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mutanen Ibo ta nemi shugaban kasa Buhari ya daina nuna kabilanci raba mukamai. Kungiyar ta roki a rika tunawa da kowa wajen wajen kason kujeru.

KU KARANTA: Ya zama dole Shugaba Buhari ya bar mulki a 2020 - PDP

Shugaban kungiyar Arewa youths Forum ta Matasan Arewa, Alhaji Yerima Shettima, da ya ke maida martani ga jawabin shugaban kasar, ya ce akwai dai bukatar kawo karshen matsalar tsaro.

Prince Uche Achi-Ogbaga wanda ya ke magana a madadin Ohanaeze Ohanaeze Ndigbo ya nemi shugaba Buhari ya daina yi wa kasar kallon Fulani da Musulmai, domin a shawo kan matsaloli.

Ita kuma PANDEF wanda ta ke da rajin kare Talakawa da Sarakunan yankin Neja-Delta ta yi kira ga shugaban kasar ya sake yi wa sha’anin tsaro garambawul ta kawo sababbin jini a gidan soji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng