Kaduna: Gobara ta kone mai jego, jariri da mutane uku a Rigasa

Kaduna: Gobara ta kone mai jego, jariri da mutane uku a Rigasa

Wutar gobara da ta tashi a wani gida dake layin Yan Tanki a unguwar Rigasa a garin Kaduna ta yi sanadiyar mutuwar wata Mai Jego, Jaririnta da sauran wasu mutane uku a gidan.

Sai dai, jama'a sun balle tagar daya daga cikin bandakan gidan tare da kubutar da mijin marigayiyar, Sani Yahaya Jumare, tare da garzaya wa da shi zuwa asibiti mafi kusa.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gobara ta tashi a gidan da misalin karfe 2:00 na daren ranar Alhamis yayin da mazaune gidan ke yin barci.

Ko a safiyar ranar Alhamis, Legit.ng ta wallafa labari mai alaka da wannan, inda hukumar kashe gobara ta jahar Kano ta sanar da tseratar da mutane 11 daga mutuwa a cikin wasu gobara guda 97 da suka auku a cikin shekarar 2019, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun hukumar, Saidu Muhammad ne ya bayyana haka inda yace sun kubutar da mutane 11 da kadarori na naira miliyan 33 daga gobara 97 da suka faru a shekarar 2019 a Kano.

Malam Saidu ya bayyana ma menema labaru hakan ne a Kano a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, inda yace mutane uku sun mutu a gobara a Kano a shekarar 2019, haka zalika an yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 15.

Ya kara da cewa a shekarar 2019, sun amsa kiraye kirayen mutane na hakikai sau 9, yayin da sun samu kiraye kirayen karya guda 10. Saidu ya bayyana sakaci wajen amfani da tukunyar girka ta iskar gas a matsayin babban abin da ya janyo gobara a Kano a shekarar 2019.

Sauran dalilan da suka haddasa gobara a jahar Kano sun hada da amfani da kayan wuta marasa inganci, amfani da na’urar dafa wuta ‘heater’, da kuma rashin iya janyo wuta zuwa cikin gida.

Daga karshe kakakakin ya yi kira ga jama’a da su guji amfani da kayan wuta ta hanyoyin da bai kamata ba, sa’annan ya shawarcesu dasu daina ajiye man fetir a gidajensu, musamman a lokacin hunturu don magance yiwuwar tashin gobara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel