Wajibi ne Buhari ya bar mulki a 2023 - PDP

Wajibi ne Buhari ya bar mulki a 2023 - PDP

Jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) mai adawa a Najeriya, ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye kalamansa na sabuwar shekara wanda a cewarta ba lallai ba ne game da nanata aniyarsa ta "rashin tsayawa takara" a 2023.

Jam'iyyar ta bayyana cewa dole ce ta sa Shugaba Buhari maimaita lamarin rashin son tsayawa takarar tasa domin kuwa ba shi da sauran zabi da ya wuce na barin mulki a karshen wa'adinsa .

A ranar Laraba, 1 ga watan Janairu ne dai shugaban kasar ya sake jadadda cewa ba shi da niyyar sake tsayawa takara a 2023, yayin jawabinsa na shiga sabuwar shekara, .

Sai dai sakataren jam'iyyar mai adawa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya ce kamata ya yi Buhari ya daina nuna tamkar yana da wani zabi na ci gaba da mulki har bayan shekara ta 2023.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole bai isa ya hana ni zarcewa ba – Gwamna Obaseki

A wani labari na aban, mun ji cewa wata babbar majalisar matasan Yarbawa a ranar Talata ta ce a cikin lumana da zaman lafiya zata soki yunkurin yankin Arewacin kasar nan na cigaba da rike shugabancin Najeriya a 2023.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa'adin mulkinsa ne nan da shekaru uku, kuma ana ta cece-kuce a kan wanne yankin kasar nan ne zai fitar da shugaban kasa.

Agbarijo Egbe Odo Yoruba tace, ta lura tare da natsewa da komai dake tashe a dangane da zaben 2023.

Majalisar tace, ta gano cewa wasu dattawa a arewa na ta shirin cigaba da rike wannan kujerar, wanda hakan ya ci karo da yarjejeniyar da aka yi a kan kujerar mulkin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel