Bayan Musayar Wuta: Rundunar 'yan sanda ta kubutar da 'yammata 6 da 'yan bindiga suka sace a Katsina

Bayan Musayar Wuta: Rundunar 'yan sanda ta kubutar da 'yammata 6 da 'yan bindiga suka sace a Katsina

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kubutar da wasu 'yammata shidda da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a kauyen Mata-Mulki dake yankin karamar hukumar Batsari.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana cewa dakarun rundunar atisayen 'Puff Adder' ne suka kubutar da 'yammatan bayan musayar wuta da 'yan bindigar da suka sace 'yammatan.

A cewarsa, 'yan bindigar sun sace 'yammatan ne ranar Talata da misalin karfe 10:23 yayin da suke aiki a gonakinsu.

"A ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, 2020, mun samu kiran gagga wa da misalin karfe 12:30pm cewa wasu 'yan bindiga da suka ki rungumar sulhu sun kai hari kauyen Mata-Mulki dake karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Bayan Musayar Wuta: Rundunar 'yan sanda ta kubutar da 'yammata 6 da 'yan bindiga suka sace a Katsina
'Yammata 6 da 'yan bindiga suka sace a Katsina
Asali: Twitter

"DPO na ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Batsa ya jagoranci jami'an tawagar 'Puff Adder' sun bi sahun 'yan bindigar har ta kai ga sun yi musayar wuta bayan sun tarfa su a wani jeji.

DUBA WANNAN: Babbar diyar marigayi Abacha ta rabu da mijinta dan kasar Kamaru

"Bayan 'yan ta'addar sun ga babu alamun samun nasara, sai suka bar 'yammatan suka gudu zuwa cikin surkukin jeji, lamarin da ya bawa jami'anmu damar kubutar da Zahara'u Abdullahi, mai shekkaru 16, da sauran wasu 'yammata da 'yan bindigar suka sace a kauyen Mata - Mulki," a cewar jawabin da Kakakin ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel