Mansurah Isah: Babbar matsalar da nake fuskanta wajen taimakawa marasa karfi

Mansurah Isah: Babbar matsalar da nake fuskanta wajen taimakawa marasa karfi

- Shugabar gidauniyar ‘Today’s Life Foundation’, Mansurah Isah ta bayyana irin nasarorin da gidauniyar ta samu tun bayan kafa ta

- Matar Jarumi kuma mawaki Sani Danjah ta ce, kalubalen da take fuskanta a wasu lokuta kan sa ta fara tunanin rufe gidauniyar da fatan wanda tayi ya hau mizani

- Tayi kira ga masu hannu da shuni da su dinga kai ziyara asibitoci ko wuraren da mabukata suke don tallafawa jama’ar Annabi

Shugaban gidauniyar tallafawa mabukata da marasa lafiya mai suna ‘Today’s Life Foundation’, Hajiya Mansurah Isah ta bayyana irin tarin matsalolin da take fuskanta a wajen aikin tallafawa jama’a. Ta ce hakan na sa wani lokacin ta ji kamar ta dakatar da wannan fafutukar, da fatan wanda tayi Ubangiji ya sanya a mizani.

Sananniyar tsohuwar jarumar Kannywood din, ta bayyana hakan ne a lokacin da take tattaunawa da mujallar fim kan irin nasarorin da gidauniyar ke samu tun bayan kafa ta.

Matar Jarumin mawaki Sani Danja, ta ce gaskiya an samu manyan nasarori tun bayan kafa wannan gidauniya, kuma dumbin mabukata sun amfana da hakan.

“Muna da bangaren samar da abincin da aka dafa ko kuma tsaba. Wannan kokarin mun yi shi a cikin birni da kauyuka, duk muna shiga domin kai wa mabukata talllafi. Bayan haka, mu kan ziyarce asibitoci domin kai wa marasa lafiya magani da kudin da zasu dan rike a hannunsu. Bangaren mata masu haihuwa da kananan yara muka fi mayar da hankali,” cewar Mansurah Isah.

Da ta juya bangaren matsalolin da suke samu kuwa, sai Mansurah ta ce, “Abin tashin hankalin da muke fuskanta shine yadda zaka ga ana hada wa mara lafiya kudi, kafin mu kammala sai kaga Allah ya dauki ranshi. Wannan abun na matukar sa ni cikin tashin hali da firgici.”

KU KARANTA: Gwamnan jihar Zamfara ya ware Naira Biliyan Daya domin gyaran Masallatai da Makabartu a jiharsa

Ta kara da cewa, “Wata matsalar itace yadda mutane ke zuwa da rashin lafiyarsu, bayan an nemi kudin ,maganinsu sai su ce su basu yadda da hakan ba. Misali shine wata yarinya mai cutar daji da aka gama hadawa kudin magani. Sai likitoci suka ce sai dai a cire hannun amma iyayenta suka ce sam basu san wannan zancen ba. Dole ta sa muka hakura tunda sune iyayenta.”

Mansurah ta ce hakan ke sa ta fara tunanin ko dai ta hakura da gidauniyar ne. Ta yi kira ga masu wadata da su dinga shiga asibitoci ko wasu wurare da ake bukatar taimako, su ga yadda mutane ke cikin yanayi na bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel