Hukuma ta ce ba a bi doka wajen ba Saraki filayen Ilorin a shekarar 1980 ba

Hukuma ta ce ba a bi doka wajen ba Saraki filayen Ilorin a shekarar 1980 ba

Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana dalilinta na karbe wasu filaye kwanakin baya a Garin Ilorin na Iyalin Marigayi Sanata Olusola Saraki.

Shugaban hukumar da ke kula da harkar filaye a jihar Kwara, Mista Ibrahim Salman, ya bayyana cewa ainihi filin na ginin sakatariya ne.

Ibrahim Salman wanda shi ne Darekta Janar na hukumar ya ce har da wurin ajiye motocin ma’aikata ya kamata a gina a wadannan filayen.

“Ainihi an karbe filin a shekarun 1970 ne bayan an danne hakkin al’umma, kuma ya kamata ace an gina sashen sakatariyar Kwara ne a wurin.”

“An fara aikin sakatariyar jihar har an soma gini kafin ayi watsi da aikin. A shekarun 1980 kuma aka canza tsarin aikin da za ayi a kan filayen.”

KU KARANTA: An karbe wani gidan tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki

Hukuma ta ce ba a bi doka wajen ba Saraki filayen Ilorin a shekarar 1980 ba
Gwamnati ta ce wasu gine-gine ya kamata ayi a filin Saraki
Asali: UGC

Ibrahim Salman ya ce: "An yi za a gina Dakin shan maganin ma’aikatan gwamnati, da sakatariya, da kuma wurin ajiye motocin ma’aikatan wurin.”

“A 1982 aka gina dakin shan magani a bangaren filin, yayin da aka bar ragowar filin domin a fadada dakin shan maganin zuwa babban asibiti.”

"Bayan an ba kamfanin Asa Investment (watau kamfaninsu Olusola Saraki) wannan fili sai gwamnati ta gaza iya gina asibitin da ta yi niyya."

Bugu da kari hukumar ta ce akwai alamun cewa game da takardun bada filayen, sannan kuma babu hujjar da ke nuna an bada kudi wajen fansar filin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel