Yan bindiga sun bindige mutane 4 har lahira a babban birnin tarayya Abuja

Yan bindiga sun bindige mutane 4 har lahira a babban birnin tarayya Abuja

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai farmaki wani gari, Kabi-Mangoro dake cikin karamar hukumar Kuje na babban birnin tarayya Abuja, inda suka bindige wata mata da wasu mazaje guda uku babu gaira babu dalili.

Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin garin mai suna Ezekiel ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi da misalin karfe 8:47 na dare a lokacin da yan bindigan suka kutsa kai cikin garin.

KU KARANTA: Jagoran yan bindiga ya bayyana yadda haduwarsa da kwamishinan Yansanda a daji ta kasance

“Koda suka shigo, sun tarar da wasu matasa zaune a kofar gidansu, a wannan lokaci ne su ka yi kokarin tserewa, daga nan suka bude musu wuta, nan take suka fadi matattu. Ita kuwa matar ta mutu ne sakamakon harbin mai kan uwa da wabi da yan bindigan suka yi.” Inji ta

Sai dai rundunar Yansandan babban birnin tarayya Abuja ta musanta mutuwar mutane hudu, inda mai magana da yawun rundunar, ASP Mariam Yusuf ta ce ba tare da bata lokaci ba aka tura jami’an Yansanda garin bayan samun rahoton shigar yan bindigan, inda suka kama yan fashi da makami guda 2 a kauyen Gbogu dake kusa da Kabi-Mangoro.

“An samu mutane biyu da suka mutu bayan yan fashin sun yi musu fashi, sa’annan suka sassaresu, sa’annan kwamishinan Yansanda ya kaddamar da binciken sirri game da lamarin domin kamo guda daga cikin yan bindigan da ya tsere.” Inji ta.

Daga karshe Kaakaki Mariam ta mika sakon jajantawa ga iyalan mutane biyun da tace sun rasa rayukansu a sanadiyyar wannan mummunan hari da yan bindiga suka kai musu har gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng