A karon farko an samu jaruma bakar fata da ta fara fitowa a fim din Indiya

A karon farko an samu jaruma bakar fata da ta fara fitowa a fim din Indiya

- Shonisani Masutha budurwa ce mai shekaru 28 daga kasar Afirka ta Kudu kuma baka da ta fara fitowa a fim din Indiya mai dogon zango

- Fim din Bollywood din mai dogon zango da Mashutha ta fito a cikin shi sunan shi Mehek

- Masutha ta bayyana cewa bata taba tsammanin zata iya fitowa a fim din Bollywood ba

Shonisani Masutha budurwa ce 'yar asalin kasar Afirka ta kudu daga Limpopo. Ta kafa tarihin zama 'yar wasan kwaikwayo baka ta farko da ta fara bayyana a fim din Indiya mai dogon zango. Kamar yadda Glamour.co.za ta bayyana, budurwar tayi nasarar samun fitowa a wannan fim din ne bayan da tayi intabiyu ta manhajar Skype.

Kamar yadda Masutha tace, bata taba tsammanin zata samu wani gurbi a masana'antar ba saboda launin fatar ta. Zama ta farko kuma baka da ta samu wannan gurbin kuwa, babbar nasara ce ga Masutha.

A kalaman budurwa mai shekaru 28 ta ce: "Gaskiya ban yi zaton ni suke nema ba. Ban kuma yi tunanin zan iya wasan kaikwayo da masana'antar Bollywood ba. Amma wakili na yace in je in gwada dai."

KU KARANTA: Tirkashi: An yankewa tsoho hukuncin daurin rai da rai akan ya saci N3,000

Wannan kyakyawar budurwar ta tuna yadda ta dinga jin tsoro yayin intabiyu kuma da yadda ta kirkiro kwarin guiwa.

A fim din Mahek, Shonisani Masutha ta bayyana a matsayin budurwa daga nahiyar Afirka da ta garzaya Indiya don neman na kanta. A yayin haka ne budurwa ta sarke da soyayya mai cike da rashin tabbas.

Shonisani Masutha tace ta koyi babban darasi a rayuwarta. "Wannan al'amarin ya nuna min cewa rayuwa zata iya karewa a inda kake kuma baka san mai ke zuwa ba matukar baka matsa ba," ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel