Ni zan zama ciwon-kan ku a shekarar nan – Fayose ya fadawa Makiya

Ni zan zama ciwon-kan ku a shekarar nan – Fayose ya fadawa Makiya

Ayodele Fayose, wanda ya yi gwamna a jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa zai cigaba da zamewa makiyansa matsala a bana.

A cewar tsohon gwamnan, muddin makiyan na sa ba su tuba ba, zai yi ta jawo masu takaici a wannan shekarar ta 2020 da aka shiga a Ranar Laraba.

Mista Ayodele Peter Fayose ya bayyana wannan ne a jawabinsa na shiga sabuwar shekara wanda ya yi a kan shafinsa na sada zumuntan zamani na Tuwita.

Ayo Fayose ya ce ya na tunanin irin tuggun da makiyansa za su kitsa masa.

Ayodele Fayose ya ce: “A wannan shekara ta 2020, Ubangiji zai ba ku galaba a kan duk wani mugu da ya addabe ku da yunwa da wahala da sauransu.

KU KARANTA: Dubi Fayose ya na tika rawa bayan ya bar Najeriya da sunan rashin lafiya

A shafin na sa na dandalin Tuwita, Jagoran na jam’iyyar hamayy ta PDP a Kudancin Najeriya ya rubuta: “Ubangiji zai kai ku kololuwar matsayi na nasara.”

“Ubangiji zai kai Najeriya ga tafarkin cigaba, zaman lafiya da hadin kai. Barka da shiga sabuwar shekara.”

Jim kadan bayan wannan sako, saki kuma ‘Dan siyasar ya rubuta:

“Har ila yau, Barka da shiga sabuwar shekara ga dukkaninmu, musamman Makiyana a siyasa da waninsa. Ina za ku ka kai ga kitsa mani tuggu? Babu ko ina.

Jawabin na sa ya kare da cewa: “Ku tuna, wanda Ubangiji ya yi wa kariya, ya fi karfin makirci. Ni ne zan zama ciwon kanku a 2020 idan ba ku tuba ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng