Maganar soyayyar Madonna Louise da Ahlamalik Williams ta yi nisa

Maganar soyayyar Madonna Louise da Ahlamalik Williams ta yi nisa

Abubuwa su na cigaba da tafiya cikin gaggawa game da soyayyar Mawakin nan Madonna Louise Ciccone da sabon Saurayinta, Ahlamalik Williams.

Miss Madonna Louise Ciccone ta gana da Mahaifin Ahlamalik Williams watau Drue Williams, ta kuma bayyana masa cewa ta na kaunar yaron na sa.

Dama can an dade ana rade-radin cewa Tauraruwar ta na bin wannan Matashi mai shekara 25, wanda ya na cikin ‘Yan rawar shararriyar Mawakiyar.

Drue ya tabbatar da soyayyar ‘Dansa da Madonna inda ya ce sun fara haduwa ne a 2015 lokacin da Yaron na sa ya nemi shiga cikin Tawagar Mawakiyar.

A lokacin da Ahlamalik Williams ya shiga jarrabawar Mazaran wannan Mawakiya ne sai ta hangesa, kuma ta zakulo shi da kanta bayan ya burge ta.

KU KARANTA: Gumsu Abacha ta rabu da Attajirin Mijinta 'Dan kasar Kamaru

Maganar soyayyar Madonna Louise da Ahlamalik Williams ta yi nisa
Madonna Louise Ciccone shararriyar Mawakiya ce kuma ‘Yar kasuwa.
Asali: Depositphotos

A watan Satumban bara, Madonna mai shekaru 61 a Duniya ta gana da Iyayen sabon Saurayin na ta a Birnin New York a Amurka, bayan ta yi wani wasa.

Daga baya kuma Madonna ta aikawa Mahaifan Ahlamalik gayyata inda ta shirya masu wata liyafa a katafaren gidanta, har ta sa aka girka masu abinci.

Mahaifin ya tabbatar da alakar, ya na cewa: “Ta (ya na nufin Madonna) fada mani cewa ta na matukar kaunar Yaro na, kuma ta na son ta kula da shi.”

Drue ya kara da cewa: “Ita soyayya babu ruwanta da shekaru. Yaro na ya na rayuwarsa ne kurum babu ruwansa.” Ya kare da cewa: “Ina yi masa murna.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel