2020: Dakarun sojojin kasa za su samu karin walwala – Janar Buratai

2020: Dakarun sojojin kasa za su samu karin walwala – Janar Buratai

Shugaban Hafsun sojojin kasa na Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya tabbatarwa Dakarun sojojin kasar na Operation Lafiya Dole karin walwala.

Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi alkawari cewa za a karawa Dakarun da ke fagen fama abin da ake ba su domin daukar dawainiyarsu.

Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana wannan ne lokacin da ya kai wa wasu Sojoji da ke Garin Pulka a cikin karamar hukumar Gwoza ziyara.

A ziyarar babban Sojan kasan zuwa Borno, ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta maida hankali game da hakkokin Dakarunta da ma Iyalansu.

Tukur Yusuf Buratai ya ke cewa: “Na san muhimmancin wannan wuri, kuma kun yi bakin-kokarin ku wajen ganin an tabbatar da tsaro a nan.”

“Saboda haka ya kamata in gode maku a kan irin wannan kokari da ku ke yi, da kuma yadda ku ke aiki a Tawagar Operation Lafiya Dole.”

“Na zo ne domin in ganku, na ziyarci sauran wurare, kuma na yi amfani da wannan dama domin in ganku kafin karshen shekara (2019)” Inji sa.

KU KARANTA: Bayanin Shugaban kasa Buhari na sabuwar shekarar 2020

2020: Dakarun sojojin kasa za su samu karin walwala – Janar Buratai

Tukur Buratai ya gana da Sojojin Operation Lafiya Dole a Borno
Source: UGC

A jawabin na san a Ranar 31 ga Disamban 2019, Janar Buratai ya kuma yi wa Dakarun na sa fatan alheri yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara.

“Mu na jinjina maku da irin jarumtar ku wajen kauda ‘Yan ta’addan Boko Haram. Dole in kuma roke ku ka kara maida hankali wajen aikinku."

“Za mu yi duk abin da za mu iya wajen ganin kun ji dadi, musamman Iyalanku da ke cikin bariki.”

“Za mu inganta walwalarku a shekarar 2020, kuma dole ku kara maida hankali, ku dage wajen rike amanar da gwamnatin tarayya ta damka maku.”

A karshe TY Buratai ya ja fadawa Sojojin su yi kokarin ganin cewa Boko Haram ba su sake dawowa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel