Dangote: Dukiyar Mai kudin Afrika ta karu da $4.3b a shekarar 2019

Dangote: Dukiyar Mai kudin Afrika ta karu da $4.3b a shekarar 2019

Jaridar Bloomberg ta kawo rahoto cewa Mai kudin Afrika watau Alhaji Aliko Dangote, ya samu karin Dala biliyan 4.3 daga cikin tarin dukiyarsa.

Aliko Dangote ya samu wannan makudan kudi ne a shekarar 2019. Attajirin ya na cigaba da samun dukiya ne wajen saida siminti da sukari.

Dangote mai shekara 62 ya kare shekarar bara da Dala biliyan 15 a lalitarsa. Wannan duk da asarar biliyan 25 da ya yi a kwanakin baya.

Ruguntsumin cinkoson da ake samu a tashar ruwan Apapa ne ya yi sanadiyyar da kamfanin Dangote ya yi asarar wannan biliyoyin kudi.

Wannan rahoto da aka fitar ya na nufin Dangote ne na 96 a jerin Attajiran Duniya. Tun Dangote ya na ‘dan shekara 21 ya fara harkar siminti.

KU KARANTA: Halima Dangote da wasu manya sun ajiye aiki a kamfanin Dangote

Dangote: Dukiyar Mai kudin Afrika ta karu da $4.3b a shekarar 2019

Aliko Dangote ya kara tashi gaba a cikin sahun Attajiran Duniya
Source: Getty Images

Dama can shekara da shekaru kenan a Nahiyar Afrika babu Mai kudin da ya iya kama kafar Aliko Dangote wanda ya fito daga Arewacin Najeriya.

Bayan siminti, Aliko Dangote ya dawo ya bada karfi wajen harkar kayan gini. Daga baya kuma ya kama layin kayan abinci har ya yi kauri-suna.

Dangote ya na da manyan kamfanoni da ke aikin sukari da fulawa. Ana zargin cewa kusancinsa da gwamnatoci kan taimakawa kasuwancinsa.

Yanzu haka Dangote ya na daf da gama gina wata matatar mai a Legas, wanda ake sa ran cewa za ta kara bunkasa karfin arzikin sa nan da lokaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel