Jama’a su na magana game da hotunan Fayose ya na holewa a ketare

Jama’a su na magana game da hotunan Fayose ya na holewa a ketare

An ga tsohon gwamna Mista Ayodele Peter Fayose na jihar Ekiti, ya na holewa abinsa a kasar waje, bayan an yi belinsa a kotu kwanakin baya.

Jama’a sun dauki hoton tsohon gwaman yayin da ya ke kwance a kan katifa, Sannan kuma an ga wasu hotunansa a cikin wani katafaren jirgin ruwa.

Ba mu da bayani game da inda aka dauki wadannan hotuna. Amma har wani bidiyo ne ya ke yawo na bidiyon Ayodele Fayose ya na rawa da wata.

Kwanakin baya ne Ayo Peter Fayose ya bukaci kotu ta ba sa damar fita kasar waje domin ya ga Likitoci a dalilin rashin lafiyar da ke damunsa.

KU KARANTA: Gwaman Jihar Bauchi zai soma biyan sabon tsarin albashi

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta na zargin Fayose da laifin wawurar Biliyan 2.2 a lokacin ya na gwamna.

A Ranar 7 ga Watan Disamban bara ne wani Alkalin babban kotun tarayya da ke Garin Legas ya ba Ayo Fayose damar fita waje ya ga Likita.

Bayan an fahimci cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti ya yaudari kuliya ne, jama’a su na ta tofa albarkacin bakinsu game da abin da ya ke faruwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel