Sai bango ya tsage: Kalli hotunan jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja

Sai bango ya tsage: Kalli hotunan jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja

Rundunar Yansandan Najeriya ta kama kan uwar gami, kuma ummul aba’isu a yunkurin fashi da makami da wasu miyagun yan bindiga suka yi a wani banki dake garin Mpape a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito Yansanda sun kama jami’in bankin da ya gayyaci yan fashin zuwa bankin nasa, mai suna Larry Ehizo dan shekara 30, wanda shi da kansa ya tuko yan fashin zuwa bankin domin su saci makudan kudade, daga baya sai su raba.

KU KARANTA: Siyasa rigar yanci: Inyamurai sun lashi takobin shugabancin Najeriya a shekarar 2023

Sai bango ya tsage: Kalli hotunan jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja

Hoton jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sauran yan fashin sun hada da Timothy Joe dan shekara 21, Princewill Obinna dan shekara 24 da Elijah David dan shekara 19. Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar din data gabata, sai dai basu samu nasara ba sakamakon Yansanda da Sojoji sun mamaye bankin.

Da yake bayyana miyagun ga manema labaru, kwamishinan Yansandan babban birnin tarayya Abuja, Bala Ciroma ya bayyana cewa suna cigaba da kokarin kamo sauran mutane biyu dake hannu cikin fashin wanda a yanzu sun ranta ana kare.

Sai bango ya tsage: Kalli hotunan jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja

Hoton jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja
Source: Facebook

“Mun kama bindigu guda biyu kirar gida a hannunsu, mota pijo 206 mai lamba SBG 752 FP, adduna biyu, wukake, wayar salula kirar Infinix, da kuma zarto daya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ebonyi ta sanar da kama wani Uba, Chinasa Ogbaga daya kashe yaransa guda biyu tare da ji ma daya mummunan rauni a kauyen Okpuitumo na karamar hukumar Abakalikin jahar Ebonyi.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Ebonyi, Loveth Odah ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin hira da ta yi da kamfanin dillancin labarun Najeriya a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel