Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala

- Jaruma Sadiya kabala a wannan shekarar ta ziyarci Saudiyya don yin umara kamar yadda ta saba

- Bayan Umararta ne ta zarce Dubai inda ta dinga shigar tsiraici kamar turawan yamma masu jajayen kunnuwa

- Ta wallafa hotunanta masu ban sha’awa cikin shigar kamala a Saudiyyan amma daga baya sai na tsiraici da tayi a Dubai suka bayyana

Jaruma Sadiya Kabala a wannan shekarar ta samu zuwa Umara kasa mai tsarki kamar yadda ta saba. Wannan ba karonta na farko bane da taje kasa mai tsarkin. Bayan kammala Umararta, bata yi kasa a guiwa ba ta zarce Dubai inda jama’a suka yi mamakin ganin yadda ta dinga shigar kamala a kasar Saudiyya, amma a Dubai ta dinga shigar Turawan yamma.

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala
Source: Facebook

Wannan shigar kuwa ta jawo cece-kuce daga ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani don kuwa sun dinga sukar shigar turawan da ta dinga yi.

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala
Source: Facebook

Amma wasu kuwa cewa suka yi jarumar na biyayya ne kawai ga wannan karin maganar da tace komai da mazauninshi, wai an sanyawa kuturu ankwa a hannunshi, ta sabule.

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala
Source: Facebook

KU KARANTA: An kama fasto a Abuja da yake sayar da man shafawa naira miliyan daya kwalba daya

Masoyan jarumar da mabiyanta a kafafen sada zumuntar zamani sun ta tofa albarkacin bakinsu a kan shigar tsiraricin da tayi. Sun yi ta cewa tafi kyau a shigar kamalar da tayi a Saudiya.

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala

Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala
Source: Facebook

Sai dai kuma jarumar ta rufe bangaren tsokaci a daya daga cikin hotunanta, hakazalika bata tankawa kowa ba a kan wannan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel