Gobara ta tashi a kasuwar Kara da ke hanyar titin Lagas-Ibadan

Gobara ta tashi a kasuwar Kara da ke hanyar titin Lagas-Ibadan

- Wasu bangarori na kasuwar Kara hanyar babbar titin Lagas- Ibadan sun kama da wuta

- Gobarar ta lalata ababen hawa da shaguna da dama a shahararriyar kasuwar dabbobin

- Zuwa yanzu mahukunta ba su ce komai ba game da abunda ya haddasa lamari ko kuma yawan asarar da aka yi

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa wasu bangarori na kasuwar Kara hanyar babbar titin Lagas- Ibadan a ranar Talata, 31 ga watan Disamba, sun kama da wuta.

Koda dai annobar ta lalata ababen hawa da shaguna da dama a shahararriyar kasuwar dabbobin, babu wani jawabin mahukunta kan abunda ya haddasa lamari ko kuma yawan asarar da aka yi zuwa yanzu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gobara ta tashi a kasuwar Kara da ke hanyar titin Lagas-Ibadan
Gobara ta tashi a kasuwar Kara da ke hanyar titin Lagas-Ibadan
Asali: UGC

Idon shaida da yan jarida sun rahoto cewa lamarin ya haddasa cunkoso sosai a hanyar babban titin.

KU KARANTA KUMA: An haramtawa Maza da Mata haduwa cikin dare a wani Gari a Jigawa

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata tankar yaki ta sojoji a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, ta kama da wuta a Damaturu, jihar Yobe inda hakan ya yi sanadiyar tashe-tashen ababen fashewa da dama daga motar.

Fashewar abubuwan ya jefa garin baki daya cikin tashin hankali yayinda mazauna yankin suka bazama domin neman kariya.

Kakakin rundunar Operation Lafiya Dole sashi na II, Kyaftin Njoka Irabor ya tabbatar lamarin.

Kyaftin Irabor ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki amma ya ce lamarin bashi da alaka da kowani hari a yankin. Ya yi kira ga mutane da su cigaba da gudanar da harkokin gabansu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel