Ba zan rusa gidan kowa wajen fadada hanyoyi ba – Inji Abiodun

Ba zan rusa gidan kowa wajen fadada hanyoyi ba – Inji Abiodun

Mai girma gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya ce gwamnati ba za ta ruguza wani gini ba, yayin da ta fara fadada titunan da ke cikin jihar.

Mista Dapo Abiodun ya bayyana wannan ne a Ranar Litinin, 30 ga Watan Disamba, 2019, yayin da ya kai wata ziyarar kewayen aikin da ake yi.

Abiodun ya duba aikin hanyar da ake yi a kan titin Ikola-Navy-Osi-AIT. Wannan hanya ta ratsa karamar hukumar Ado-Odo zuwa Otta a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa zai yi kokari wajen ganin an kammala yankin titin da ya hada jihar Ogun da kuma Legas wanda su ke makwabtaka.

Da ya ke magana a jiyan game da yin hanyoyin wucewar mutane a gefen titi, Abiodun ya ce hakan na bukatar a rusa wasu gine-ginen jama'a.

KU KARANTA: Gwamnoni da-dama ba su fara biyan sabon albashin Ma'aikata ba

Ba zan rusa gidan kowa wajen fadada hanyoyi ba – Inji Abiodun
Gwamna Abiodun ya fasa ruguza gidaje wajen barka hanyoyi
Asali: UGC

Mai girma gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ba ta shirya rusa wasu gine-gine domin a samu wurin da jama’a za su rika tafiya a gafen titin ba.

“Mun zo ne mu duba wannan aikin da ya kai matakin karshe. Al’ummar Garin su na cewa za su fi so ayi hanyar wucewar mutane a gefe.” Inji Abiodun.

“Sai dai, dole mu ka yi watsi da wannan duk da mun sa shi cikin tsarin ginin, domin ba mu so mu ruguza ginin wani, mu jawo masa bakin ciki.”

“Za mu kaddamar da titin wanda tsawon fadinsa mitoci bakwai ne, dauke da hanyar ruwa.”

Tsohon ‘dan majalisar yankin, Sanata Akin Odunsi da Mai martaba Onikotun na kasar Ottun-Otta, Oba Abdulhakeem Odunaro sun yabawa wannan aikin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel