Wa’adin 2019 zai cika amma Gwamnoni ba su karkare batun kara albashi ba

Wa’adin 2019 zai cika amma Gwamnoni ba su karkare batun kara albashi ba

Jaridar Daily Trust ta na ganin babu mamaki a buge da sabon yajin aiki ganin cewa kadan daga cikin jihohin kasar nan ne su ka kammala magana a kan karawa ma’aikata albashi.

Hukumar ‘Yan kwadago na kasa, NLC ta sa Ranar 31 ga Watan Disamba a matsayin wa’adin karshe da za a karkare duk wata zama game da shiri da fara biyan sabon tsarin albashi.

Jaridar ta ce a binciken da ta yi, ta gano cewa a Jihohi biyar ne kurum aka fara aiki da sabon albashin N30, 000. Wadannan jihohi su ne Kaduna, Legas, Adamawa, Kebbi da Jigawa.

Kawo yanzu ana tsakiyar tattaunawa ne da kungiyoyin kwadago a jihohi 17 na fadin kasar. Jihohin da magana ta yi nisa sun hada da Filato, Ekiti, Delta, Abia, Enugu, da irinsu jihar Imo.

Abin da zai tada hankali shi ne akwai jihohi 17 da har yanzu ba a kai ga kafa kwamitocin da za su duba batun sabon tsarin albashi ba. Ribas, Osun, da Benuwai su na cikin wannan sahu.

KU KARANTA: An fara biyan sabon tsarin albashin N30, 000 a jihar Kano

Yau ce dai ranar karshe a shekarar nan ta 2019 watau wa’adin da ma’aikata su ka bada ya na daf da karewa. Tuni da Gwamnatin tarayya ta soma biyan wasu ma’aikata bashin karin da ta yi.

A wata hira da ‘Yan jaridar, shugaban kungiyar ‘Yan kwadagon na Yankin Abuja, Kwamred Abubakar Alhassan Yakubu, ya kara tabbatar da barazanar tafiya yajin aiki a jihohin kasar.

Abubakar Alhassan Yakubu ya bayyana cewa babu wanda zai iya bada tabbacin zaman lafiyan ma’aikata muddin gwamnatocin jihohi su ka gaza cika alkawarin da aka yi da su a baya.

Shugaban ‘Yan kwadagon ya kuma shaidawa ‘Yan jarida cewa a birnin tarayya, lamarin ma’aikatan ya sha ban-ban, domin majalisar FEC ta amince a fara biyan sabon albashin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel