Wata sabuwa: An cire dokar raba maza da mata a kasar Saudiyya

Wata sabuwa: An cire dokar raba maza da mata a kasar Saudiyya

- Kasar Saudiyya ta fidda sanarwar daina raba tsakanin maza da mata a kasar

- Kasar ta bayyana hakan ne a kokarin da take na kawo sababbin canje-canje na zamani a kasar da kuma watsi da tsofaffin dokoki

- Kasar ta bayyana cewa daga yanzu duk wurare da ake raba tsakanin maza da mata su daina, sannan kuma kasar ta janye dukkanin askarawa dake yawo akan tituna suna sanya mutane bin ka'idojin addinin Musulunci

Kasar Saudiyya ta bayyana cewa daga yanzu ta daina raba maza da mata a wajen shiga gidajen abinci.

Kasar ta fito da wannan sabuwar dokar ne domin kawo wani sabon sauyi a harkar nishadi kamar dai yadda ta canja wasu abubuwan a baya.

Ana tunanin hakan wata hanya ce ta sassauta dokokin da suka raba hulda tsakanin maza da mata.

Gwamnatin kasar Saudiyyan ta rubuta a shafinta na Twitter: “Daga yanzu ba dole ba ne rabe-raben kofar shiga ta maza da kuma ta mata a gidajen sayar da abinci, dama duka sauran wuraren da maza da mata zasu iya haduwa.”

Tun shekara daya ko biyu da suka gabata aka fara samun sauyi, ta yadda wuraren sayar da abincin suka daina saka shamakin gilashi dake raba tsakanin maza da mata ko da kuwa mata da miji ne.

KU KARANTA: 'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya

Banda wannan sabuwar dokar kuma an ce yanzu an daina ganin jami’an tsaro na hukumar Hisbah da suke yawo domin tilasta bin dokokin addinin Musulunci sau da kafa.

Hakan dai wata alama ce dake nuni da cewa kasar Saudiyyar ta daura damarar kawo sauye-sauye akan dokoki masu tsauri da addinin Musulunci ya gindaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel