'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya

'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya

- Yana da matukar wahala ka samu mace musamman a yankin mu na kasar Hausa wacce take goyon bayan mijinta akan yayo mata kishiya

- To sai dai wani abin mamaki shine yadda muka ci karo da wani labari na wata mata mai jarumta da kokari

- Matar dai ta tilasta mijinta akan ya yo mata kishiya, inda har ta dauki nauyin bayar da gudummawa da kuma biyan kudin shagalin bikin baki daya

Zai yi wahala mata ta ga mijinta yana biye-biyen mata taji bata kishi, domin kuwa farkon abinda ke fara zuwa zuciyarta shine, ko ya daina sonta ko kuma ya gaji da zama da ita.

Shin me kuke tunanin matar za ta yi idan kawai taga mijinta ya shigo mata da sabuwar mata ba tare da saninta ba?

Tabbas a wannan ranar Allah ne kawai zai raba mijinta da amaryar tsakaninsu, domin kuwa duk kishin duniya sai ta kare shi a kansu.

'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya

'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya
Source: Facebook

Sai dai yau kuma mun ci karo da wani labari mai ban mamaki, domin kuwa wata mata ce ta goyawa mijinta baya akan ya auro mata kishiya, abin ba wai a iya nan ya tsaya ba, domin kuwa matar da kudinta ta zare ta biya duka kudin hidimar bikin har aka kare, inda ta kai da har a wajen shagalin bikin uwargidan ta fito ta bawa amaryar abinci a baki.

Wannan lamari dai ya bawa mutane matukar mamaki, musamman ‘yan Najeriya Hausawa, inda har wasu ke cewa idan har haka ta faru to ko dai mijin yana da dan karen kudi wanda uwargidan ba ta so tayi asara idan ta nuna kishi.

'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya

'Yar Aljannah: Uwargida ta bawa mijinta makudan kudade ya karo mata kishiya
Source: Facebook

KU KARANTA: Dole a kamo kuma a hukunta wadanda suka kai mini hari gidana - Jonathan

Wasu kuma suka ce akwai yiwuwar mijin yana gamsar da uwargidan matuka idan sunje kwanciyar bacci. Wasu kuwa cewa suka yi akwai yiwuwar uwargidan ta gama shiri tsaf tana jira amaryar ta shigo ta fara juya ta.

Wani kuwa cewa yayi tunda har Musulunci ya halatta auren mace fiye da daya to uwargidan bata da wata hanya sai dai tayi hakuri ta dauki kaddara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel