Zargin bin Yarima a-sha-kida: 'Yar Majalisa ta ce ba zaman Buhari su ke yi ba

Zargin bin Yarima a-sha-kida: 'Yar Majalisa ta ce ba zaman Buhari su ke yi ba

Wata mamba a majalisar wakilai, Honorable Wumi Ogunlola ta yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa majalisar dokoki na tara yan a bi yarima a sha kida ne, inda ta jadadda cewa ba dukkanin bukatun Shugaban kasa Muhammadu Buhari yan majalisar ke yin na’am dashi ba.

Yar majalisar, wacce ke wakiltan mazabar Ekiti ta tsakiya ta bayyana cewa an zabe su ne domin su yi wakilci domin jama’ar mazabunsu da kuma aiwatar da dokokin da za su kawo gwamnati mai inganci, inda ta kara da cewa ya zama dole dukkanin bangarorin gwamnatin guda biyu su yi aiki cikin aminci domin kasar ta samu dukkanin cigaba.

Da take jawabi ga manema labarai a Ijero-Ekiti a ranar Lahadi, Ogunlola ta yi bayanin cewa ya zama dole yan Najeriya su guji auna kokarin majalisar dokokin kasar da adadin lokutan da suke kin amincewa da shugaban kasar cewa maimakon haka kamata yayi su auna shi da cigaba da ingancin dokokin da suke aiwatarwa.

KU KARANTA KUMA: Don Allah ka nada ni shugaban hukumar INEC – Injiniya Buba Galadima ga Buhari

A cewar yar majalisar ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC), "Bana tunanin duk abunda ya shigo majalisar dokoki daga bangaren zartarwa ake amincewa dashi, hakan ba daidai bane.

"Idan kun san abunda suke kawowa da abunda ake mayar masu, imma yi masu ragi ko kari, abun ba daya bane, hakan na nufin majalisar dokokin kasar ta dauki wasu matakai."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel