Gasar Firimiya: Ba zan kashe kai na a kan Arsenal ba – Inji Atiku Abubakar
Sanin kowa ne a yanzu cewa harkar kwallon kafa ya girmama sosai ta yadda ba wai yara ko matasa bane kadai ke goyon bayan kungiyoyin kwallon kafa ba, a’a, har ma da manyan mutane, kamar yadda Atiku Abubakar ya tabbatar.
Ga wadanda basu sani ba, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar na daya daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake taka leda a gasar Firimiya na kasar Ingila.
KU KARANTA: Jerin wasu zafafan wakokin Hausa 10 da suka burge jama’a a cikin shekarar 2019
Sai dai Atikun bai ji da dadi ba bayan kungiyar Arsenal ta sha kashi a karshen makon da ta gabata, inda kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa ta ci biyu da daya, daidai da abin da masu iya magana ke ce ma ‘Tsiyar nasara sai za shi gida.’
Farawa da iyawa dan wasan Arsenal Aubameyang ya zuwa kwallo a ragar Chelsea a minti na 13, da wannan Atiku ya rubuta a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Twitter: “Kwallo mai kyau, Aubameyang”
Sai dai yayin da ake gab da kammala wasan, sai Chelsea ta zura kwallaye biyu cikin mintuna 5 ta hannun Jorginho da Tammy Abraham, wannan yasa dan Atiku, Mustapha Atiku Abubakar ya fada ma babansa cikin raha: “Baba ya kasuwa?”, inda Atikun ya bashi amsa “Ba zan kashe kai na, kamar yadda Timaya yake fada.”
Timaya dai wani shahararren mawaki ne daga kudancin Najeriya, wanda ya yi fice, kuma a shekarar 2019 ya fitar da wata bakandamiyar wakarsa mai suna ‘I can kill my self”, ma’ana “Ba zan kashe kai na ba.”
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng