Babbar magana: Na yaudari samari da dama, amma nima kuma an yaudare ni - Rayya

Babbar magana: Na yaudari samari da dama, amma nima kuma an yaudare ni - Rayya

- A wata hira da fitacciyar jarumar tayi wacce tauraruwar ta ke haskawa a wannan lokacin wato Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya

- Ta bayyana wasu muhimman abubuwa game da rayuwarta, irin su shekarunta da kuma lokacin da ta fara fim

- Haka kuma a wata tambaya da wakilin freedom rediyo yayi mata, akan ko ta taba yaudara a rayuwarta, jarumar ta amsa da eh ta taba yi

Awata tattaunawa da tayi da gidan rediyon freedom, Jarumar mai tasowa Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya ta cikin shirin kwana casa’in, ta amsa wasu muhimman tambayoyi da suka shafi harkar sana’arta da kuma rayuwarta.

Jarumar wacce keda shekaru 22 a duniya ta bayyana cikakken suna da adadin shekarunta da kuma lokacin da ta shigo cikin harkar fim.

Cikin wasu tambayoyi da wakilin gidan rediyon ya yi mata a gurguje, ya tambayeta ko ta taba soyayya a zahiri ta bayyana cewa kwarai ta taba yi.

Haka ya kara tambayarta ko an taba yaudarar ta, jarumar ta bada amsa da cewa duk inda akwai soyayya to akwai yaudara, saboda haka an yaudareta.

Ya cigaba da tambayarta, ko shin ita ma ta taba yaudarar wani, sai kawai ta bushe da dariya ta ce eh kwarai kuwa na taba yi.

KU KARANTA: Azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da kuma kariya daga cututtuka - Cewar Masana a Amurka

A karshe jarumar ta bayyana cewa bata da wani ubangida a Kannywood, kuma burinta shine ta zama shahararriya ba wai a iya Najeriya ba, a duniya baki daya.

Haka kuma da aka sake dauko mata zancen aurenta ta bayyana cewa a kasuwa take tunda ita dai budurwa ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng