An kama wani saurayi da ya dane tayar jirgin sama a lokacin da yake shirin tashi a filin jirgin sama na Legas

An kama wani saurayi da ya dane tayar jirgin sama a lokacin da yake shirin tashi a filin jirgin sama na Legas

An kama wani saurayi yayinda ya ke kokarin danewa tayar wani jirgin sama na kamfanin Air Peace da ke zuwa Owerri a filin jirgin sama na Lagas.

A cewar kakakin kamfanin jirgin, Stanley Olisa, saurayin ya fito ne daga dajin da ke hanyar wajen ajiye jirage na filin jirgin sannan ya yi kokarin danewa tayar jirgin lokaccin da yake shirin tashi.

Olisa ya ce matukin wani jirgi wanda ya sanar da jami’an tsaro da ke aiki tare da hukumar kula filin jirgin saman Najeriya (FAAN) ne ya sanar da ainahin matukin jirgin da yake shirin danewa, sannan jami’an tsaro suka tisa keyar saurayin..

A wani jawabi a ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba, Air Peace tace: “A safiyar yau, da misalin karfe 9:10 na safe a filin jirgin sama na MMA 1 Lagas,jirgin Air Peace (flight P47252) mai zuwa Owerri na shirin tashi, sai wani saurayi ya fito daga dajin da ke kusa da wajen tashin, sannan ya yi kokarin shiga jirgin ta cikin tayarsa.

"Akwai wani jirgi mai zaman kansa a bayan jirgin. Sai matukin jirgin ya sanar a matukin jirgin na Air Peace cewa wani saurayi na kokarin shiga jirgin.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka yi cushen naira biliyan 264 cikin kasafin kudin 2020 da Buhari ya sa hannu

“Sai aka sanar da jami’an tsaro da ke aiki da hukumar FAAN sannan suka kama mutumin suka tafi dashi. A yanzu haka yana tsare a hannun masu kula da filin. Da aka tambaye shi kan dlilinsa na daukar wannan mataki, mutumin ya bayyana cewa ya zata jirgin zai tafi kasashen waje ne. Mun yaba ma FAAN akan shiga lamarin da tayi cikin gaggawa. Ana kan binciken lamarin.

“Air Peace na cigaba da jajircewa domin tsare kwastamominta kuma za ta cigaba da nuna wannan jajircewar a dukkanin ayyukanta. A kamfanin Air Peace, tsaro shine jigon abuna muke yi.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng