An yi ram da Sowore ne saboda kokarin tada-zaune-tsaye ba don ya na ‘Dan Jarida ba

An yi ram da Sowore ne saboda kokarin tada-zaune-tsaye ba don ya na ‘Dan Jarida ba

Sa’o’i kadan bayan Jagoran tafiyar nan ta RevolutionNow, Omoyele Sowore, ya koma gida, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba ta kama shi a matsayinsa na ‘Dan jarida ba.

A cewar fadar shugaban kasar, ta bakin Malam Garba Shehu, hukuma ta damke Omoyele Sowore ne a dalilin yunkurin da ya ke faman yi na kawowa gwamnatin Najeriya matsala.

Malam Shehu ya ce akwai bukatar ayi wa Duniya wannan jawabi domin wasu gidajen jaridun kasar waje su na tunanin aikin jaridarsa ta sa Tele Sowore ya shiga hannun jami’ai.

Garba Shehu ya ce tun daga lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki zuwa yanzu, bai taba kama wani ‘Dan jarida ko ya kai wa wani kamfanin gidan jarida hari ba.

Mai magana da bakin shugaban na Najeriya ya ke cewa laifin Sowore shi ne kiran ayi wa gwamnati mai-ci bore. Shehu ya ce gwamnatin Buhari ta na bin dokar Najeriya.

KU KARANTA: Jami'an DSS sun hana Sowore wayoyinsa bayan sun sake shi

Mai magana da bakin shugaban kasar ya ke cewa: “Tun da Buhari ya shiga ofis a 2015, bai taba kama wani ‘Dan jarida ba, ko ya karbe jaridu, ko ya rufe wata gidan jarida.”

“Sowore ya yi kira ne na kifar da gwamnatin da aka zaba a Najeriya, ya yi wannan ne a gidan talabijin, a matsayinsa na wanda ya mallaki kafar yada labarai a Amurka.

“Sowore ya kirkiro tafiyar RevolutionNow ne wanda ke da nufin tada hankali da kifar da gwamnati. Babu gwamnatin da za ta zura idanu ana yunkurin hargitsa kasa.

Gwamnatin Buhari ta ce ta yi imani da bin dokar kasa, amma dole ta tsare al'umma, ta ce ba za ta bari wasu mutane su zuga jama’a har a kai ga kawo tashin hankali ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel