Siyasa mugun wasa: An cigaba da tone tonen asiri tsakanin manyan gwamnanonin PDP 2

Siyasa mugun wasa: An cigaba da tone tonen asiri tsakanin manyan gwamnanonin PDP 2

Tsatstsamar dangantakar da ta taso tsakanin manyan gwamnonin jam’iyyar PDP na shiyyar kudu masu kudancin Najeriya na cigaba da fitowa fili, inda gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike ya zargi takwaransa na Bayelsa da kokarin komawa jam’iyyar APC.

Wike ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labaru a fadar gwamnatin jahar Ribas dake garin Fatakwal, inda yace Gwamna Seriake Dickson na jahar Bayelsa ya kammala shirin komawa jam’’iyyar APC tsaf, amma karamin ministan mai, Timipre Sylva ya dakile shirinsa.

KU KARANTA: A raba kowa ya samu: El-Rufai ya baiwa Kaakakin majalisar Kaduna rikon jahar Kaduna

Shi dai Sylva babba ne a jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Bayelsa, wanda sau biyu yana neman sake komawa kujerar gwamnan, amma sau biyu Gwamna Dickson yana fyada shi da kasa.

Haka zalika Wike ya zargi Dickson da yi ma APC aiki a zaben gwamnan jahar da ta gabata wanda dan takarar APC ya lashe, inda yace gwamnan ya ci amanar jam’iyyarsa ta PDP ne don kawai tsoron abinda hukumar EFCC za ta iya masa.

“Ina sane da cewa Dickson ya kammala shirin sauya sheka zuwa APC, amma Timpre Sylva da Heineken Lokpobiri suka dakile shi, ya san ina da karfi, ai daya tuntubeni, ya hada baki da mutanen nan ne don gudun kada EFCC ta kama shi idan ya sauka.

“Idan ka ga dam aka yi ta yada farfaganda son ran ka, amma a shirye nake na kare muradun jahar Ribas, ta yaya Dickson zai iya kama jahar Ribas bayan ya gaza wajen kare jahar Bayelsa?” Inji shi.

Idan za’a tuna a rahoton na baya mun shaida muku yadda Dickson ya zargi Wike da kokarin raba kawunan al’ummar kabilar Ijaw, biyo bayan wata ziyara daya kai ma babban basaraken Ijaw na jahar Bayelsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng