Na koma Legas da zama ne saboda na ceci rayuwata - Adam A Zango

Na koma Legas da zama ne saboda na ceci rayuwata - Adam A Zango

- Jarumi Adam Zango ya bayyana cewa ya koma Legas da zama saboda harkar fim ta ruguje a Arewa

- Ya bayyana cewa nan da watanni shida ko zuwa shekara daya zai kwashe iyalinshi su koma can

- Ya bayyana cewa, a halin yanzu yana kokarin kulla alaka da shahararrun mawakan Kudancin Najeriya

A zantawar da jaridar mako-mako ta Aminya tayi da jarumin Adam Zango, ya bayyana cewa harkokinshi a Legas sun kankama. Yana shirin nan da watanni shida zuwa shekara zai mayar da iyalinshi gaba daya da mahaifiyarshi Legas.

A hirar da wakilin fim magazine din yayi da jarumin, Zango ya bayyana cewa tunda ya kai kololuwa a harkar fim a Arewa, to abu mafi dacewa shi ne ya koma Kudu da zama domin harkokinshi zasu fi ci a can

Ya ce, “Kamar dalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare, idan yana so ya ci gaba da karatunshi sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami’a.”

Wani dalilin da jarumin ya bada shine, Legas gari ne da ake samun kudi sosai.

“Legas gari ne na samun rufin asiri, idan mutum na so ya samu rufin asiri mai nauyi toh Legas zai nufa.” in ji shi.

KU KARANTA: Budurwa ta saka saurayinta ya kashe tsohuwar budurwarsa don ya tabbatar da soyayyarsa a gareta

Jarumin ya bayyana yadda lamurran masana’antar Kannywood ke tabarbarewa a kullum. Ya yi kira ga jama’a mazauna kudancin kasar nan da su yi mishi maraba tare da rungumarshi hannu bibbiyu. Ya bukacesu da su ringa gayyatarshi bukukuwa ko tarukansu don ya dinga nishadantar dasu.

“Kamar dai yadda suka sanni da nishadantarwa, toh nesa ta zo kusa. Zasu iya gayyatata don nishadantar dasu a bukukuwa ko tarukansu.”

Jarumin na da tabbbacin cewa kakarshi zata yanke saka. Don kuwa a halin yanzu ya ce yana kokkarin kulla dangantaka da manyan mawakan kudu guda biyar. Sun hada da Davido, Burna Boy, Tekno, Olamide da Lighter. Amma jarumin ya tabbatar da cewa, duk abinda zai yi a Kudu ba zai bari ya taba mutuncinshi ba da na addininshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel