Buhari ya goyi bayan sulhu tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II

Buhari ya goyi bayan sulhu tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya goyi bayan wani kwamiti mai karfin gaske da aka kafa domin dinke barakar da ke tsakanin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Jaridar Solacebase dake Kano ta bayyana cewa sakataren kwamitin, Wazirin Fika, Alhaji Adamu Fika, ya sanar da ita cewa an kafa kwamitin ne a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya).

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa kungiyar dattawan Arewa wacce ake kira da 'Northern Elders Forum (NEF)', ta fara wani taro domin sasanci a tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Buhari ya goyi bayan sulhu tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II

Ganduje da Sarki Sanusi II
Source: Twitter

Dattawan sun yi yunkurin sulhu tsakanin Gwamnan da Sarkin ne bayan da Sarkin ya amince da nadin da gwamnan Kano yayi masa, na shugaban majalisar sarakunan jihar.

Sanusi ya amince da nadin ne bayan da aka aike masa da wasikar neman ko dai ya amince ko kuma akasin hakan, biyo bayan shirun da ya yi tun farko.

Dr. Hakeem Baba Ahmed na kungiyar NEF ya shaida wa BBC cewa, kasancewarsu dattawa, ba dai-dai bane suna ganin wannan lamarin na faruwa, kuma su ja bakinsu su yi shiru.

DUBA WANNAN: Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan Aliko Dangote da kudin da aka kashe

Da yawan masu nazarin al'amura sun bayyana cewa gwamnatin Kano ta kirkiri sabbin masarautun ne domin rage karfi da ikon sarki Sanusi, saboda sukar gwamnatin Ganduje da yake yi.

Sai dai, a nasa bangaren, Ganduje ya kafe a kan cewa ya kirkiri sabbin masarautun ne domin samun yaduwar cigaba zuwa kowacce kusurwa ta jihar Kano.

Kafin kirkirar sabbin masarautun Bichi, Karaye, Gaya da Rano, sarki Sanusi II ne kadai sarkin yanka a jihar Kano, lamarin da yasa ya nuna adawarsa ga kirkirar wasu sabbi dake zaman tamkar kishiyoyi a gare shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel