Karar kwana: Yadda Amarya da 'yan rakiyarta 21 suka mutu a hatsarin mota

Karar kwana: Yadda Amarya da 'yan rakiyarta 21 suka mutu a hatsarin mota

Marigayi Alhaji Abdullahi Buwa yana daga cikin dattijan Fulani da suka jagoranci sauran Fulani da zasu raka sabuwar amarya, Daharatu, zuwa dakin mijinta a Yola, jihar Adamawa, bayan kammala shagulgulan biki daga kauyensu dake yankin karamar hukumar Dutsin-Ma a jihar Katsina.

Kazalika, an dora wa Alhaji Buwa nauyin raka wata amaryar mai suna Nafisatu zuwa dakin mijinta, daga Yola, amma haka bata yiwu ba sakamakon hatsarin motar da ya sanadiyar mutuwarsa da sauran 'yan tawagarsa da suka bar Katsina tare zuwa Adamawa.

An kammala shagulgulan biki cikin farin ciki a Karofi ranar Alhamis, a cikin makon jiya, inda daga nan aka wuce tashar mota dake Dustin-Ma aka dauki hayar babbar motar daukan fasinja da zata dauki amarya da dattijan da zasu raka ta zuwa Yola.

An yi bikin auren ne bisa al'adar Fulanin ta shekara - shekara da ake kira "Gidan Dangi"; inda Fulanin daga ke ziyartar kauyukan da aka haifi kakanninsu a Yola.

Sai dai, al'adar ta zo da abun bakin ciki da tashin hankali bayan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar dukkan 'yan uwa da dangin amarya da suka tafi domin yi mata rakiya zuwa dakin miji da kuma gudanar da sauran al'amuransu na al'adar Fulanin Yola.

Domin kara wa bikin al'adar na shekarar 2019 armashi, kabilar Fulanin da ke zaune a Yola da na jihar Katsina sun kulla auratayya a tsakaninsu, inda kowanne bangare ya auro kuma ya aurar.

A cikin jawabin da ya fitar, akakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Abubakar, ya ce hatsarin ya afku ne a kusa da kauyen Gubi dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano tare da bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon 'taho mu gama' da motar 'yan bikin ta yi da wata mota kirar J5 dake dauke da mutane hudu da shanu 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel