Taraba: Darius Ishaku ya rabawa sababbin Kwamishinoninsa Ma’aikatu

Taraba: Darius Ishaku ya rabawa sababbin Kwamishinoninsa Ma’aikatu

Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ya rabawa sababbin Kwamishinoninsa da ya zaba ma’aikatun da za su rike. Gwamnan ya raba ofishoshin ne a Ranar 19 ga Watan Disamban 2019.

Idan ba ku manta ba, Mai girma gwamnan na jihar Taraba ya zakulo Kwamishinoni 25 da zai yi aiki da su ne a karo na biyu. Hakan na zuwa kusan bayan watanni bakwai da ya koma kan mulki.

Kamar yadda mu ka ji, Dr. Badina Garba shi ne zai rike Ma’aikatar lantarki. Taninga Binga zai kula da ma’aikatar ayyuka na musamman. Solomon Elisha ya zama Ministan tattali da tsare-tsare.

Adamu Ibrahim shi ne Ministan sufuri da harkokin jiragen sama. Edward Baraya zai kula da ma’aikatar ilmin na gaba da sakandare, Naphtali H. Kefas ya na ma'aikatar kawar da talauci.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya taba manyan Sakataororin Gwamnatin Tarayya

Jesse Adi shi ne Ministan kudi, inda alhakin yada labarai ya rataya a kan Anyeze Adamu. Sabon Kwamishinan harkar lafiya na jihar shi ne Innocent Vakkai. Sam B. Adda zai lura da shari’a.

Ma’aikatar ruwa ta na hannun Yusuf Akirikwen. Aliyu Dankaro shi ne zai kula da ma’aikatar gidaje. Joseph Obadiah Asseh shi ne sabon Kwamishinan ziyarar shakatawa na jihar Taraba.

Wanda zai rike Ma’aikatar raye karkara shi ne Alexander M. Senlo. Sauran Kwamshishinonin jihar sun hada da Alhassan Hamman, kimiyya da Yusuf Tanimu Njeke a Ma’aikatar kasuwanci.

Bridget Twar, Joha Jigem, da David Ishaya za su rike Ma’aikatar ilmi, noma da cigaban al’umma. Sai kuma Irimiya Hamman, Yusuf Njeke, Ibrahim Lawan, Ibrahim Imam da Hauwa Kwenna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel