Kasafin kudi: Buhari ya kafa sabon tarihi - Gwamnonin APC

Kasafin kudi: Buhari ya kafa sabon tarihi - Gwamnonin APC

- Gwamnonin jam'iyyar APC sun ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa sabon tarihin da tun da aka dawo mulkin dimokraddiya babu wani shugaba da ya kafa shi

- Wannan shine karo na farko a tarihin Najeriya da wani zababben shugaban kasa ya saka hannu a kan kasafin kudin sabuwar shekara tun kafin shigowarta, a cewar gwamnonin

- Kungiya gwamnonin ta taya shugaban kasa murna tare da jinjina wa shugabancin majalisar kasa bisa yin aikinsu bisa tsarin dokar kasa da kuma kishin 'yan Najeriya

Gwamnonin jam'iyyar APC sun ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa tarihi a bangaren kasafin kudi bayan ya rattaba hannu a kan kasafin kudi, tiriliyan N10.594, na shekarar 2020 kafin a fita daga shekarar 2019.

Gwamnonin, a karkashi kungiyar PGF (Progressive Governors Forum), sun ce shugaba Buhari ya kafa sabon tarihin da tun da aka dawo mulkin dimokraddiya, kimanin shekaru 20 da suka gabata, babu wani shugaba da ya kafa shi.

A cewar PGF, wanna shine karo na farko a tarihin Najeriya da wani zababben shugaban kasa ya saka hannu a kan kasafin kudin sabuwar shekara tun kafin shigowarta.

Kasafin kudi: Buhari ya kafa sabon tarihi - Gwamnonin APC
Buhari yayin rattaba hannu a kan asafin kudin 2020
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar PGF kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a cikin jawabin taya Buhari samun wannan gagarumar nasara da ya yi a tarihin gwamnati da mulkin Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

Kungiyar ta taya shugaban kasa murna tare da jinjina wa shugabancin majalisar kasa ta bisa yin aikinsu bisa tsarin dokar kasa da kuma kishin 'yan Najeriya.

A cikin sanarwar, kungiyar PGF ta bayyana cewa a shirye take koda yaushe domin bayar da gudunmawarta da goyon baya wajen tabbatar da cewa an samu fahimtar juna a tsakanin dukkan bangarorin gwamnatin tarayya da jihohi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel