Bauchi: Kotu ta zartar da hukunci a kan matashin da ya kashe mahaifinsa a Masallaci

Bauchi: Kotu ta zartar da hukunci a kan matashin da ya kashe mahaifinsa a Masallaci

Wata babbar kotun jihar Bauchi ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani matashi, Umaru Jauro Ori, bayan samunsa da laifin kisan mahaifinsa a cikin Masallaci a kauyen Mai'aduwa dake yankin karamar hukumar Misau a jihar Bauchi.

Alkalin kotun, Jastis Aliyu Usman, ya ce ya yanke wa matashin hukuncin kisa ne bayan sauraron shaidu da kuma jawabin bangaren masu kara da wanda aka gurfanar.

A hukuncin da ya zartar, Jastis Usman ya ce, "masu kara sun tabbatar tare da kore duk wani shakku a kan cewa wanda ake kara ne ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, A saboda haka wannan kotu ta same shi da laifin aikata kisa, laifin da aka tanadar wa laifi a karkashin sashe na 221 na kundin shari'a. Na yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

Yayin da ake sauraron karar, lauya mai gabatar da kara, Hussein Magaji, ya sanar da kotu cewa Jauro ya shiga har cikin Masallaci ya kashe mahaifinsa ta hanyar datsa masa adda a ka da kuma bayansa.

Bauchi: Kotu ta zartar da hukunci a kan matashin da ya kashe mahaifinsa a Masallaci

Bauchi: Kotu ta zartar da hukunci a kan matashin da ya kashe mahaifinsa a Masallaci
Source: UGC

Lauyan ya kara da cewa marigayin ya samu munanan raunuka sakamakon saran da Jauro ya yi masa, lamarin da yasa aka garzaya da shi babban asibitin garin Misau, inda washegari ya mutu saboda rasa jini mai yawa.

DUBA WANNAN: Kotu ta jaddada karfin ikon Ganduje na tumbuke sarakunan jihar Kano

Alkalin kotun ya bayyana cewa da farko Jauro ya musanta tuhumar zargin kisan kan da ake yi masa kafin daga bisani lauya mai gabatar da kara ya kira shaidu 10 da suka tabbatar wa rundunar 'yan sanda a cikin jawabinsu cewa shine ya kashe mahaifinsa.

Umar Jatau, wani dan uwa ga mamacin ya shaida wa kotun cewa akwai matsala a tsakanin Jauro da mahaifinsa da kuma tsakaninsa da saura mutanen dangi.

A jawabinsa ga rundunar 'yan sanda, Jauro ya bayyana cewa yana da mata da yara uku, tare da bayyana cewa ya kashe mahaifinsa ne saboda ya raba aurensa da matarsa yayin da ya yi wani bulaguro mai tsawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel