Yan bindiga sun bude ma jami’an kwastam wuta, 2 sun mutu

Yan bindiga sun bude ma jami’an kwastam wuta, 2 sun mutu

Hukumar yaki da da fasa kauri ta kasa, reshen jahar Neja ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyu a hannun wasu gungun yan bindiga da suka kai musu farmaki yayin da suke bakin aiki a kan iyakar jahar Neja da jahar Kwara.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa kwanturolan kwastam mai kula da shiyyar Neja da Kwara, Abba Kassim ne a tabbatar haka yayin da yake tattaunawa da ita kamfanin, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Cika shekaru 77: Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa

A cewar Kassim, da misalin karfe 10 na daren Alhamis ne yan bindigan suka yi ma jami’an hukumar kwastam kwantan bauna yayin da suke gudanar da sintiri a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene.

Daga cikin jami’an hukumar da suka mutu akwai ASP S.Ohiremen da ASP S.M Omale, sai kuma wani jami’i guda daya daya samu rauni a sanadiyyar bude wutan da yan bindigan suka yi, DSP H.I Oladapo.

“Mun yi bakin ciki matuka da mutuwar wadannan jami’ai namu, kuma tuni aka garzaya da jami’in daya samu rauni zuwa babbar cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Lokoja domin samun kulawa.

“Za mu cigaba da aiki tukuru da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da mun gano gungun yan bindigan da suka kai mana harin, tare da kamosu da hukuntasu kamar yadda doka ta tanada.” Inji shi.

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta kaddamar da bincike a kan wasu makudan kudade har naira biliyan 14.8 da suka yi batan dabo daga lalitar hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam.

Kwamitin majalisa mai kula da asusun gwamnati ne ya kaddamar da bincike biyo bayan korafi da mai binciken kudi na kasa yayi game da kudaden hukumar kwastam, inda yayi zargin akwai lauje cikin nadi game da binciken kudi da aka yi ma kwastam a tsakanin shekarun 2013 da 2014.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel