Mutanen da suka yi wakar 'Buhari Jirgin Yawo' sun azabtu a hannun wani dan siyasa

Mutanen da suka yi wakar 'Buhari Jirgin Yawo' sun azabtu a hannun wani dan siyasa

- Mawakan da suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wakar 'Buhari Jirgin Yawo' sun ga ta kansu

- Mawakan anyi musu dukan kawo wuka a jihar Kebbi bayan sun je sunyi wakar cin mutunci ga wani dan siyasa tare shugaba Buhari

- An bayyana cewa har gida aka je aka ciccibo mawakan aka kai su gidan wani dan siyasa a nan garin Birnin Kebbi

Wasu mutane da ake zargin 'yan bangar siyasa ne, sun je garin Gwadangaji dake jihar Kebbi da misalin karfe 2 na dare, suka yi awon gaba da mawaki Bello Bala Aljannare daga gidansa.

Rahotannin da jaridar Dabo FM ta bayar ya bayyana cewa mutanen sun wuce da mawakin zuwa gidan wani dan siyasa a cikin garin Birnin Kebbi dake jihar ta Kebbi.

Bayan kai shi gidan anyi masa dukan kawo wuka, ciki harda yi masa barazanar kisa, kamar yadda ya shaidawa Dabo FM.

Haka zalika da misalin karfe 3 na dare aka je wani otal aka balle kofar shi aka shiga aka fito da sauran mawakan dake ciki aka wuce da su zuwa gidan dan siyasan.

Bayan kai su gidan suma an yi musu dan karen duka kamar dai yadda aka yiwa Bello Aljannare.

KU KARANTA: Abin yayi yawa: An kama 'yar fim da take kwanciya da miji sannan kuma tayi madigo da matarshi

Rahotanni sun nuna cewa na yiwa mawakan wannan dukan tsiya ne bayan wata waka da suka yi ta cin mutuncin wani dan siyasa a jihar Kebbi tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan lamari dai ya tada hankulan mutane ganin yadda cikin kwanaki kalilan dumbun mutane sun mallaki wannan wakar da mawakan suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel