Kotun Legas ta na neman Tauraron Mawaki Naira Marley a kan zargin sata

Kotun Legas ta na neman Tauraron Mawaki Naira Marley a kan zargin sata

A Ranar Litinin, 16 ga Watan Disamba mu ka ji cewa Wani karamin Kotun Majistare da ke Garin Legas, ya bada umarni a cafko masa wani Mawakin Najeriya mai suna Mista Adeyemi Fashola.

Jama’a sun fi sanin wannan shawararren Mawaki da Naira Marley. Kotu ta ce ta na neman sa ne da zargin ya na da hannu a satar wata mota da kuma wayar salula da aka yi a cikin Garin Legas.

Jami’in kotun, Tajudeen Elias, ya umarci jami’an tsaro su kawo Mawakin gaban kuliya a zaman da za ayi na gaba. Kotu ta sanar da ‘Dan Sandan da ke binciken lamarin ya kawo mata Mawakin.

Wasu ‘Yanuwan Mawakin na jini watau Idris Fashola, Babatunde Fashola, da Kunle Obere, duk sun hallara a kotu a zaman da aka yi, ana zarginsu da laifin sata da kuma hana a kama Mawakin.

Idris Fashola ‘dan shekara 18, da Yayansa Babatunde Fashola mai shekaru 24 duk Kannen Mawakin ne. Shi kuma Mista Kunle Obere mai shekara 22 a Duniya, ‘Danuwansu ne na jini.

KU KARANTA: Jami’ar Abuja ta sallami Malamin da ya ke neman mata

Ana zarginsu da laifuffuka da su ka hada da Mauje wani Bawan Allah da kutun-kutun da kuma yunkurin hana jami’an tsaro su cafke Naira Marley. Wannan duk sun sabawa dokokin jihar Legas.

ASP Edet Okoi, ya fadawa kotu cewa wadannan Matasa uku sun aikata laifin ne a otel din Eko da ke Unguwar Victoria Island. Sun yi wannan ne a lokacin da su ke tare da Mawaki Naira Marley.

Sun saci wata mota samfurin Toyota Camry da lamba FEE 120 AA wanda kudin ta ya kai Naira miliyan 1.8. Sun kuma sacewa wani Adelekan Ademola wayar Iphone X5 wanda ta N330, 000.

Lokacin da wannnan Mutumi ya nemi ya kawo kukan a dauke masa kaya, sai su ka yi masa duka, sannan kuma su ka hana Jami’an ‘Yan Sanda su cafke Mawakin. Yanzu an bada belinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel