Kwamacala: Uba ya auri 'yar cikinsa bayan sun shafe shekaru suna soyayya

Kwamacala: Uba ya auri 'yar cikinsa bayan sun shafe shekaru suna soyayya

- Wata mata ta bayyana wani abu da ya gigita mutane a kafafen sada zumuntar zamani

- Ta wallafa hotonta da na mahaifinta inda ta yi bayanin cewa, daga uba da ‘ya, sun koma miji da mata

- A daya daga cikin hotunan, ya bayyana yadda suke sumbatar juna da mahaifinta kamar ma’aurata

Wata mata ta bayyana yadda ta fara soyayya da mahaifinta kuma suka yi aure. Matar mai suna Jimi Meaux a Facebook ta bayyana tsohon hotonta tare da mahaifinta wanda suka dauka lokacin da take yarinya. Ta kara da bayyana wani hotonta tare da mahaifin nata inda take sumbatarsa a matsayinshi na mijinta.

A kasan hoton ta rubuta, “Mun fara matsayin mahaifi da ‘ya, mun kare a matsayin mata da miji. Wani lokacin, mahaifanka ne masoyanka.

Ai kuwa wannan wallafar ta jawo cece-kuce daga ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani na Facebook da na Tuwita. Ga kadan daga cikin tsokacin da jama’a suka dinga:

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwar da take biya kanta kudin makaranta ta hanyar yin aikin gini ta kammala karatun ta na jami'a

”Wannan abun ya cika da ban mamaki. Wannan sumbar ta makusanta juna ce. Na rasa me zance.” In ji Zoya.

Areajulid kuwa cewa ya yi: “Tabbas iyaye masoya ne amma banda irin wannan soyayyar. Abun amai.”

PreMota kuwa ya wallafa; “Ki yi bayani dalla-dalla a kan wannan abun da kika rubuta ‘Wani lokacin iyayenka ne masoyanka.’"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel