Jam’iyyar APC ta dage dakatarwar da ta yi ma Rochas, da gwamnan jahar Ondo

Jam’iyyar APC ta dage dakatarwar da ta yi ma Rochas, da gwamnan jahar Ondo

Uwar jam’iyyar APC ta dage matakin ladabtarwa na dakatarwa da ta yi ma gwamnan jahar Ondo Rotimi Akeredolu, tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha da tsohon gwamnan jahar Ogun Ibikunle Amosun.

Jaridar The Cables ta ruwaito kaakakin jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, inda yace baya ga gwamnonin, APC ta yafe ma tsohon minista Usani Uguru Usani da shugaban kamfanin muryar Najeriya, Osita Okechukwu.

KU KARANTA: Rai ba’a bakin komai ba: Miyagu sun banka ma wata Mata wuta a Abuja

Kaakaki Onilu yace manufar jam’iyyar ta wannan yafiya shi ne domin yi ma mutanen adalci tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar, baya ga nuna cewa babu wani dan jam’iyya da yafi karfin jam’iyya.

“Muna fatan mutanen da abin ya shafa zasu yi amfani da wannan dama wajen daidaitawa da jam’iyyar a matakin mazabarsu, kananan hukumominsu da kuma uwar jam’iyyar a jaharsu, tare da cigaba da baiwa jam’iyya gudunmuwa don ganin an cimma gaci.” Inji shi.

Jam’iyyar APC ta sallami wadannan mambobi nata ne gabanin babban zaben shekarar 2019 sakamakon zarginsu da cin dunduniyar jam’iyya da kuma rashin da’a da biyayya ga uwar jam’iyyar.

A wani labarin kuma, hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani mutumi daya shahara a wajen tafka mummunan dabi’ar damfara, Malik Wakili, da laifin damfarar minista kuma tsohon gwamnan jahar Legas.

EFCC ta tasa keyar Wakili gaban kotu ne bisa zarginsa da damfarar ministan ayyuka da gidaje a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola naira miliyan 3.1.

A ranar Litinin, 16 ga watan Disamba ne jami’an EFCC suka gurfanar da wannan gagararren dan damfara gaban babban kotun tarayya dake karkashin Alkali Mai Sharia Chukwujekwu Aneke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel