Jaruma Rahama Sadau ta bude gidan shan shisha a Kaduna

Jaruma Rahama Sadau ta bude gidan shan shisha a Kaduna

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bude gidan kwalliya mai suna ‘Sadau Home’ a Kaduna. Tun farko dai jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa zata bude sabon waje mai suna ‘Sadau Home’ a Kaduna.

Ta kira wajen da ‘wurin da ya kamata ka je a Kaduna.' Jarumar dai ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta karo na 26.

A Sadau Home, akwai bangaren shan Shisha wanda ya ja hankulan ‘yan Arewacin kasar nan.

Kamar yadda ma’anar Shisha take, kalma ce a harshen larabci mai nufi da kwararo na kona taba. Wannan bangaren na shan Shisha kuwa, ya ja hankulan sanannun ‘manyan yara’ na kasar nan.

DUBA WANNAN: Shugabannin kasashen Afrika 7 da suka mallaki manyan kudade

A cikin kwanakin nan, da yawa daga cikin taurarin masana’antar sun bazama duniyar kasuwanci. Sun hada da Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Sani Danja da sauransu.

A yayin tsokaci a kan bude wajen shan Shisha da Rahama Sadau ta yi, Muhsin Ibrahim, malami ne a jami’ar Cologne da ke kasar Jamus, ya ce: "Lokaci ya yi da zamu gane cewa, jaruma Rahama Sadau ba ta damu da abinda mutane ke cewa a kanta ba. Duk yadda muka dauka wajen shan Shisha; dai-dai ko akasin hakan, matukar zai amfaneta bata damu ba. Shisha dai ta matasa ce, kuma al’ada ce ta birni. Wajen shan Shishar Sadau ta matasa ce.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel