Shugabannin kasashen Afrika 7 da suka mallaki manyan kudade

Shugabannin kasashen Afrika 7 da suka mallaki manyan kudade

7. Idriss Déby (miliyan $50)

An haifi shugaban kasar Chad, Idriss Derby, a shekarar 1952 kuma tun shekarar 1990 yake mulkin a kasar har yanzu. Ya lashe zaben kujerar shugaban kasa a Chad har sau biyar.

Jaridar 'Forbes' ta lissafa kasar Chad a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da matalar cin hanci ta yi tsanani, saboda fiye da mutum miliyan goma a kasar na fama da matsanancin talauci.

6. Isaias Afwerki (miliyan $100)

An haifi Isaias Afwerki a shekarar 1946 a garin Asmara dake kasar Aritre kuma tun a shekarar 1993 ya hau mulki. An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $100.

5. Abdel Fattah el-Sisi(miliyan $185)

A shekarar 2014 ne Abdel Fattah el-Sisi ya zama shugaban kasar Masar (Egypt). An haife shi a shekarar 1954. Ya shiga jerin sahun mutane 50 masu karfin iko a duniya da jaridar 'Forbes' ta fitar a shekarar 2018.

An yi kiyasin cewa shugaban kasar na Egypt y mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $185. The 'Guradian' ta ce el - Sisi ya gaji mafi yawan arzikin da yake da shi daga gidansu.

4. Sarki Mswati III (miliyan $200)

Sarki Mswtai III ne ke mulkin kasar Swaziland a yanzu haka. Jaridar Forbes ta yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $200. Wasu rahotanni sun nuna cewa basaraken ya tara dukiyarsa ne daga sana'o'i da kasuwancin da yake yi da kuma dumbin hannayen jarin da ya mallaka.

Ya mallaki manyan motocin alfarm amsu tsadar gaske irinsu 'Maybach' wacce aka bayyana cewa kudinta ya kai $500,000 da kuma jirginsa da kudinsa ya kai dala miliyan $17.

A cewar wani rahoto, matan aure da 13 Sarki Mswtai III keda su sun kashe miliyan $6 a sayayyar kwalam a iya shekarar 2019.

Fiye da kaso 40% na mutanen kasar Swaziland basu da aikin yi.

3. Cyril Ramaphosa (miliyan $450)

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya kasance daga cikin mutane 12 masu arziki a kasar tun kafin ya zama shugaban kasa. Dama can shi dan kasuwa ne da aka yi kisayin cewa yana jagorantar wani kamfani dake da karfin tattalin arziki da ya kai miliyan $900.

Jaridar Forbes ta bayyana cewa Ramaphosa ya mallaki miliyan $450 a shekarar 2015. Kazalika, jaridar 'Time Magazine' ta saka sunan Ramaphosa a cikin mutane masu karfin iko a shekarar 2019.

2. Paul Kagame (miliyan $500)

A shekarar 1957 aka haifi shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, a garin Tambwe Ruanda-Urundi, sannan ya zama shugaban kasa a shekarar 2000. An yi kiyasin cewa ya mallaki miliyan $500.

Jaridar 'Financial Times' ta rawaito cewa Kagame da iyalinsa sun mallaki mafi yawan kasuwancin kasar Rwanda tare da bayyana cewa ya boye mafi yawan dukiyarsa a kasashen Turai da sunayen 'ya'yansa.

1. Uhuru Kenyatta (miliyan $500)

An haife shi a shekarar 1961 kuma shine shugabane shugaban kasa na 4 na jamhuriyar kasar Kenya, sannan kuma mahaifinsa shugaba na farko.

An yi kiyasin cewa ya mallaki dalar Amurka miliyan $500. Ya gaji afi yawan arzikinsa daga wurin mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel