Gwamnati za ta karbe filaye da gonakin Yari, Yarima, Shinkafi da ke kan kasar kiwo

Gwamnati za ta karbe filaye da gonakin Yari, Yarima, Shinkafi da ke kan kasar kiwo

Mun ji cewa tsofaffin gwamnonin jihar Zamfara da wasu 'yan siyasan jihar, da kuma manyan Sarakuna, su na gaf da rasa gonakinsu masu tsada da ke kan filayen kiwon dabbobi a jihar.

Hakan na zuwa ne bayan Mai girma gwamna Bello Muhammad Mutawalle ya bada umarni a karbe duk wani fili da ke kan layin kiwon dabbobi. Wannan zai kashe wutar rikicin da ke jihar.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wasu manyan jihar Zamfara da su ka karbe wadannan filaye da aka kebe domin Makiyaya za su rasa dukiyoyinsu. Wani jami’in gwamnatin jihar ya fadi haka.

Masu mulki ne su ka fanshi filayen, su na amfani da su. Daga cikinsu akwai Abdulaziz Yari, Mahmud Shinkafi, Ahmad Sani Yarima. Akwai kuma tsohon Kakakin jihar, Sanusi Garba Rikiji,

Sauran Kwamishinonin da wannan doka za ta shafa sun hada da Alhaji Dankande Gamji da Abdulsalam Magami. Haka zalika dokar za ta taba wasu Sarakuna da aka tsige kwanakin baya.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: Matawalle ya karbe filayen makiyaya a Zamfara

Gwamnati za ta karbe filaye da gonakin Yari, Yarima, Shinkafi da ke kan kasar kiwo
Rikicin Makiyaya ya sa Gwamnan Zamfara zai karbe filayen wasu manya
Asali: Facebook

Wadannan Sarakuna su ne na kasar Dansadau, Bakura da Gumi. Rahoton ya ce duk sun mallaki abin da ya haura eka 50 daga cikin filin da ya kamata ace dabbobi su na amfani da su wajen kiwo.

“Misali tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya mallaki fiye da eka 200 na wani fili da keg aba da Talata Mafara kafin ka karasa Kauyen Lambar Bakura, a kan babban titin Sokoto zuwa Gusau.”

Jami’in gwamnatin ya ce: “Filin tsohon gwamna Yariman Bakura ya na gefen na Yari. Gonar wani ‘Danuwan yari da ake kira Kayaye ya na kan titin na zuwa Gusau a gaba da Lambar Bakura”

Muttaka Rini ya mallaki filin eka 400 a Dansadau, Yari ya na da filin eka 1000 yayin da irinsu Sarkin Dansadau su ke da filin eka 200 a Kauyen. Akwai dai tarin filaye a hannun manyan kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel