Wuce gona da iri: Jama'a ya kamata mu fara tausayawa Rahama Sadau - Datti Assalafiy

Wuce gona da iri: Jama'a ya kamata mu fara tausayawa Rahama Sadau - Datti Assalafiy

- Bayan bayyanar wasu hotuna da bidiyo na jaruma Rahama Sadau mutane sunyi caa akanta, inda wasu ke tofin Allah tsine, wasu kuma suke yi mata addu'ar shirya

- Jarumar dai ta bayyana a cikin wata shiga ta nuna tsiraici, inda take tikar rawa da mawakin gambarar zamanin nan wato Classiq

- Classiq shine mawakin da yayi sanadiyyar dakatar da ita a shekarun baya, bayan sunyi waka tare an nuno shi yana rungumar ta

A cikin makon nan ne dai wasu hotuna suka bayyana na fitacciyar jaruma wacce take cin lokacin ta a yanzu wato Rahama Sadau, inda ta bayyana ita da wannan mawakin da suka yi waka kwanakin baya da tayi sanadiyyar dakatar da ita a masana'antar Kannywood, wato Classiq.

An bayyana jarumar cikin shiga ta kaya da suke bayyana surar jikinta, sannan aka nuno ta tana tikar rawa tare da wannan mawakin a wajen bikin bude wajen sayar da abincin ta mai suna Sadauz Home.

Wuce gona da iri: Jama'a ya kamata mu fara tausayawa Rahama Sadau - Datti Assalafiy
Wuce gona da iri: Jama'a ya kamata mu fara tausayawa Rahama Sadau - Datti Assalafiy
Asali: Facebook

Hotunan dai sun karade ko ina a shafukan sada zumunta inda mutane da dama suka dinga tofa albarkacin bakinsu, amma mafi yawancin mutanen suna yiwa jarumar addu'ar neman shiriya ne.

Bayyanar wannan hotunan ya sanya fitaccen mawallafinan na shafin Facebook wato Datti Assalafiy yayi dogon rubutu akan jarumar mai taken 'Ya kamata mu tausayawa Rahama Sadau'.

KU KARANTA: El-Rufai yana daya daga cikin mutanen dana ji dadin aiki da su a lokacin mulkina - Obasanjo

Ga dai abinda ya rubuta: "Rahama Sadau a mizani na cigaban mai hakan rijiya, hajarta sai kara gaba keyi, duniya ta aureta sosai, siffarta ta Musulunci har ta fara canjawa, ina matukar jin tausayin wannan baiwar Allah.

"Duk lalacewar wasu daga cikin matan da suke sana'a irin nata Musulmai, iskancinsu bai kai ga fara bayyana da irin wannan mummunar shiga ta rashin mutunci alhali suna amsa sunan Musulunci ba.

"Abinda take yi ba wayewa bane, kuma ba abin burgewa bane, ya kamata a tausaya mata, sannan ayi mata addu'a, a dinga jan hankalin iyaye mata Musulmai da kada suyi sha'awar rayuwar duniya irin wannan, ko 'yan boko aqeedah da suke ingizata basa barin kannensu mata suna bayyana da irin wannan mummunar shigar.

"Ya Allah ga baiwarka nan, Allah kai ka halliceta, Ya Allah muna rokonka ka shiryeta, idan ba mai shiryuwa bace Allah ka nesanta wannan dabi'a tata ga sauran Musulman Najeriya baki daya amin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel