Daga shekarar 2023 za mu daina shigo da man fetir daga kasashen waje – Shugaban NNPC

Daga shekarar 2023 za mu daina shigo da man fetir daga kasashen waje – Shugaban NNPC

Gwamnatin tarayya ta sanya shekarar 2023 a matsayin lokacin da za ta daina shigo da man fetir wanda aka tace daga kasashen waje gaba daya, domin tana sa ran zuwa lokacin matatun man fetirin Najeriya sun mike tsaye.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin da yake rattafa hannu kan yarjejeniyar tsarin samar da kananan matatun mai a Najeriya da zasu dinga samar da litan tataccen mai miliyan 20.

KU KARANTA: Uwargida Aisha ta koka kan rashin samun lokacin yin soyayya da Buhari yadda ya kamata

Kasar Najeriya dai ta dogara ne da tataccen man da ake shigo mata da shi daga kasashen waje wanda take sayar ma yan kasa don amfanin yau da kullum sakamakon dukkanin matatun man kasar guda hudu sun daina aiki.

A jawabinsa, Mele Kyari, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damu matuka kan yadda Najeriya ta zamto kasar da ta fi kowacce kasa sayan man fetir duk da cewa tana daga cikin kasashen da suka fi arzikin dan mai a duniya.

Sai dai ba wannan bane karo na farko da gwamnatin ta sanya ranar daina shigo da man fetir daga kasashen waje, domin kuwa a shekarar 2017 ma gwamnatin Buhari ta taba sanya shekarar 2019 a matsayin shekarar da za ta daina shigo da mai, amma sai ga shi kuma ta sake tsawaita lokacin.

A wani labarin kuma, ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Ehanire ya koka kan hauhawan yan Najeriya dake sha tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi, don haka yayi kira ga shuwagabannin makarantu da iyaye su zage damtse wajen magance matsalar.

Ministan yace wadannan rukunin yan Najeriya suna amfani da akalla daya daga cikin wadannan kayan shaye shaye; tabar wiwi, hodar iblis, kwayoyi da kuma miyagun allurai akalla sau daya a shekara daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel