Kalaman Aisha Buhari sun tabbatar da Buhari cikakken dan siyasa ne – Yahaya Bello

Kalaman Aisha Buhari sun tabbatar da Buhari cikakken dan siyasa ne – Yahaya Bello

Gwamnan jahar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba dan kama karya bane, cikakken dan siyasa ne wanda har a cikin gidansa, tsakanin iyalansa ma siyasa yake bugawa.

Jaridar The Cables ta ruwaito Bello ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da yayi da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

KU KARANTA: Mummunan hatsarin mota ya lakume mutane 28 yan gida daya a jahar Bauchi

A cewar Yahaya Bello: “Shugaba Buhari ne mutumin da na sani mafi iya siyasa kuma halastaccen dan dimukradiyya, wannan ne karo na farko da muka taba ganin tsohon shugaba na mulkin Soja ya rungumin tsarin dimukradiyya har a cikin gidansa, balle kuma a kasar.”

Idan za’a a yan kwanakin nan an jiyo uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari tana ta babatu tare da sukar kumfar baki a kan zargin zagon kasa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu yake mata, inda ta bayyana shi a matsayin mutum mai fuska biyu mara biyayya.

Sai dai da yake magana game da rahoton da ake yadawa na cewa wai babban mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Janar Babagana Munguno ya bayyana zaben Kogi da Bayelsa a matsayin abin da hankali ba zai dauka, Bello ya mayar da martani kamar haka;

“Ba na jin Munguno ya fadi wannan magana, na san haka saboda zaben da aka yi a jahar Kogi yayi daidai da muradin jama’an jahar. Idan kace hankali ba zai dauka ba, eh na yarda, saboda ba’a taba tunanin zan iya zama gwamna a yadda na zama ba, amma Allah Ya kawo ni.

“Hankali ba zai dauka ba saboda wannan ne karo na farko da karamar kabila ta taba cin zabe a jahar Kogi, haka zalika wannan ne karo na farko da muka rage matsalar kabilanci a jahar Kogi, kuma wannan ne karo na farko da muke ririta kudin gwamnati tare da hana sata.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel