Ramin karya kurarre ne: Yar uwar Abdulrashid ta tona masa asiri a gaban Alkali

Ramin karya kurarre ne: Yar uwar Abdulrashid ta tona masa asiri a gaban Alkali

Masu iya magana suna cewa “Ramin karya kurarre ne”, wannan shi ne kwatankwacin abin da ya faru a zaman babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba inda ake sauraron shari’ar tsohon shugaban kwamitin yi ma dokokin fansho garambawul, Abdulrashid Maina.

Idan za’a tuna dai EFCC ta maka Maina gaban kotun ne kan zarginsa da satar akalla kudi naira biliyan 2, tare da mallakar kadarori da dama, wanda take zargin duk ya samesu ne ta hanyar kwashe kudaden talaka yan fansho a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Jigawa za ta kashe naira miliyan 60 wajen gina dakunan ‘ba haya’

Sai dai a zaman kotun na ranar Laraba, reshe ya juye da mujiya saboda idan Maina ya raina fata bayan wata kanwarsa Fatima Abdullahi da yake amfani da sunanta wajen bude kamfanoni da kuma boye kudade a bankuna ta tona masa asiri.

Fatima, wanda ma’akaciyar gwamnati ne ta bayar da shaida ne a boye, ta yadda Alkalin kotun, mai sharia Okon Abang ne kadai ke iya ganin fuskarta, amma kowa dake kotun yana jin sautin muryarta, inda ta tabbatar ma kotun cewa uwarsu daya ubansu daya da Maina, amma bata da masaniya da duk abubuwan da yake yi.

Ta musanta mukamin Darkata da aka ce tana rike da shi a wnai kamfanin da Abdulrashid Maina ya bude, kamar yadda ya yi rajistan kamfanin da sunanta, ta tabbatar ma kotun cewa ba da ita aka bude asusun bankin wani kamfani mai suna Common Input and Drew da bankin UBA ba.

Haka zalika ta bayyana ma kotu cewa sunan da aka yi amfani da shi wajen rajistan kamfanin, Fatima Samaila Abdullahi, ba sunanta bane, domin sunanta Fatima Abdullahi kawai, haka nan hoton da aka yi amfani dashi, hotonta ne tun tana budurwa, haka nan sa hannun da aka gani a rajistan ba nata bane.

Daga karshe dai Fatima ta tabbatar ma kotu cewa bata da hannun jari na ko sisi a cikin wadannan kamfanoni da Maina ya saka sunanta a ciki, don haka can ga su gada. Bayan nan sai Alkalin kotun ya dage karar zuwa ranar 16 ga watan Disamba.

Wannan yasa masu bibiyan bahallatsar Maina suke ganin lamar kamar irin yadda zaka ga masu kudi basu taimakon yan uwansu, amma saboda son kai sai su yi amfani da sunansu wajen satar kudaden jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel